Dubban jama’a ne suka mamaye manyan ƙauyuka da hanyoyin da ke kaiwa garin Ɗansadau domin tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a wata ziyara ta tarihi da ya kai yankin. A ranar Laraba ne gwamnan ya ziyarci al’ummar Ɗansadau da ke Ƙaramar Hukumar Maru, ziyara da ta ɗauki hankalin …
Read More »Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na 58 A Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar karo na 58 tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, abin da gwamnatin jihar ta ce ya zama wani muhimmin tarihi a tafiyar shugabancinsa. A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci wannan zama na 58 a zauren …
Read More »Zamfara Ce Ta Ɗaya A Yankin Arewa Maso Yamma A Fannin Cibiyoyin Kula Da Lafiya A Matakin Farko
Jihar Zamfara ta zama zakara a fannin kula Cibiyoyin kula da kiwon lafiya a matakin farko a duk faɗin yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan. Sunan Zamfara ya fito ne a lokacin wani taron karramawa na Hukumar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko PHC, wanda ya gudana a …
Read More »Tinubu Ya Miƙa Lambar Karramawa Ta Ƙasa Ga Gwamna Dauda Lawal
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya damƙa Lambar Karramawa ta Ƙasa a Ayyukan Hidimta wa Al’umma (NEAPS) 2025 ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa ayyukan da gwamnati ta gudanar waɗanda suka sauya tsarin mulki da tsaro a jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata …
Read More »Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 mai darajar Naira Biliyan 861 ga Majalisar Dokokin Jihar, inda ya bayyana shi a matsayin taswirar sauyi da kuma shaida cewa Zamfara na kan hanyarta ta tashi tsaye da ƙarfi. An gabatar da kasafin ne …
Read More »Tinubu Ya Zaɓi Gwamna Dauda Lawal Cikin Tawagar G20 A Afirka Ta Kudu
Daga Imrana Abdullahi Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kasance cikin gwamnonin da aka zaɓa domin raka Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu zuwa taron Shugabannin Ƙasashe 20 (G20 ) da za a gudanar a Afirka ta Kudu. Taron, wanda za a yi ranar 22 da 23 ga Nuwamba, zai tattaro …
Read More »Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu -Gwamna Lawal
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa samun lambar yabo ta “Gwamna Mafi Nagarta Na Shekara” daga jaridar LEADERSHIP babban ƙarfafawa ce gare shi domin ci gaba da gudanar da ayyuka masu tasiri ga al’ummar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi takardar sanarwar kyautar …
Read More »Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
Daga Imrana Abdullahi Jihar Zamfara ta samu babban ci gaba a fannin gudanar da harkokin kuɗi, inda rahoton BudgIT ya nuna cewa jihar ta haura daga matsayi na 36 a 2023 zuwa matsayi na 17 a 2025, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal. Wannan sabon rahoto na 2025 State of …
Read More »Gwamnatin Zamfara Ta Warware Matsalar Ɗaliban Ta Da Aka Bari A Indiya
Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Zamfara (ZSSB) ta bayyana cewa Gwamnan Jihar, Dauda Lawal, ya amince da biyan bashin kuɗin karatun ɗaliban jihar da suka yi karatu a Jami’ar Sharda da ke ƙasar Indiya. Wannan mataki, a cewar hukumar, ya zama wani muhimmin ci gaba wajen cika alƙawarin gwamnati …
Read More »Gwamna Lawal Ya Jagoranci Taron Majalisar Zartarwa, Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaƙi da matsalolin tsaro a jihar aiki ne na haɗin kai da ya rataya a wuyan kowa da kowa, ba na gwamnati kaɗai ba. A ranar Litinin, gwamnan ya jagoranci zama na 18 na Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a Gidan …
Read More »
THESHIELD Garkuwa