Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya damƙa Lambar Karramawa ta Ƙasa a Ayyukan Hidimta wa Al’umma (NEAPS) 2025 ga Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa ayyukan da gwamnati ta gudanar waɗanda suka sauya tsarin mulki da tsaro a jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya wakilci shugaban ƙasa a wajen taron cin abinci na karramawar da aka shirya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, kamfanin The Best Strategic Media ne tare da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne suka shirya wannan gagarumin taro da tun 2022 ake gudanarwa domin gano shugabanni masu hazaƙar aiki da gaskiya da tasiri a faɗin ƙasa.

Sanarwar ta ce, an zaɓi Gwamna Lawal ne saboda yadda gwamnatinsa ta kawar da ƙalubalen da suka daɗe suna ci wa ma’aikatan Zamfara tuwo a kwarya.
Daga cikin abin da ya fi ɗaukar hankali akwai biyan tsohon bashin giratuti da ya wuce naira biliyan 15 — bashin da ma’aikata suka ɗauki kusan shekara 13 suna jira. Haka kuma gwamnatin ta tashi tsaye wajen farfaɗo da jin daɗin ma’aikata, ta ɗaga mafi ƙarancin albashi daga N7,000 zuwa N70,000, sannan ta dawo da albashin wata ta 13 a matsayin kyautatawa ga ma’aikatan gwamnati.
A fannin ci gaban al’umma, gwamnatin ta nuna cewa dubban ayyuka sun gudana a lokaci guda: daga sabunta tituna da tsabtace garuruwa, zuwa gyaran makarantun gwamnati fiye da 500 da inganta manyan asibitoci a dukkan ƙananan hukumomi.
Haka kuma an jaddada nasarorin tsaro, musamman kafa Rundunar Tsaron Al’umma ta Community Protection Guards, sayen sabbin motocin sintiri da kayayyakin aiki, da tallafin da gwamnati ke ba jami’an tsaro a kullum.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan lambar girmamawa ta NEAPS za ta ƙara wa Gwamna Lawal ƙaimi wajen ci gaba da aikin sake gina Zamfara ta fuskar gudanarwa, tsaro, da jin daɗin al’umma.
THESHIELD Garkuwa