Daga Imrana Abdullahi
Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wasu muhimman nade – naden mukamai.
Ya zabi Sanata George Akume,a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Juma’a 2 ga watan Yuni, 2023.
Ga abubuwa bakwai game da Akume ku sani
Akume, wanda aka haife shi a ranar 27 ga watan Disamba, 1953, ɗan asalin gundumar Wannune Tarka ne na Jihar Banuwai.
A shekarar 1978 ya kammala karatunsa na digiri na farko a fannin zamantakewa a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo. Haka kuma jami’ar ta ba shi digiri na biyu a fannin masana’antu da hulda da ma’aikata a shekarar 1986.
Akume ya zama Gwamnan Jihar Banuwai daga watan Mayu 1999 zuwa Mayu 2007 kuma a Jihar Banuwai shi ne gwamna na farko da ya yi wa’adi na biyu cikakku
Sannan, daga watan Yunin 2011 zuwa watan Yunin 2015, ya zama cikin jerin shugabannin Majalisar Dattawa.
A dan takaitaccen lokaci da ya yi a majalisar dattawa tsohon Gwamnan ya taba zama shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji.
Sanata Orke Jev na jam’iyyar PDP ne ya kada shi a zaben 2019 domin zama dan majalisar dattawa.
Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa, ya nada George a matsayin ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati a ranar 21 ga Agusta, 2019.