Home / Labarai / Tsaro Ne Babban Kudirin Mu A Jihar Kaduna – Jonathan Asake

Tsaro Ne Babban Kudirin Mu A Jihar Kaduna – Jonathan Asake

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Labo (Labour) Honarabul Jonathan Asake ya bayyana batun tsaro a matsayin al’amari na farko da zai dauki mataki a kansa idan jama’a suka zabe shi Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa manema labarai a Kaduna sa’ilin da ya ziyarci cibiyar yan jarida ta kasa NUJ reshen Jihar.
Jonathan Asake ya ce a halin da ake ciki manoma ba su iya zuwa Gonakinsu saboda matsalar tsaron da ake fama da ita.
“Akwai wasu makarantu da dama da duk sun kulle a halin yanzu suk sakamakon matsalar tsaron da ake fama da ita, kai akwai wasu kamfanoni a Jihar Kaduna da duka kwashe kayansu daga cikin Jihar suka koma wata Jiha domin matsalar da ake da uta ta tsaro, da akwai wasu kuma masu kokarin zuba karin da suka kasa yin katabus wanda sakamakon hakan duk sun canza Jiha.
Masu Garkuwa da satar jama’a duk suna neman mamaye ko’ina da ina, idan kuma sun kama mutane sai su bukaci wasu kayayyaki kamar Babura, kudi da wasu kayayyaki, kai har cewa jama’a suke aje wuri kaza inda ake sayar da Baburan aje wurin wane domin za su gaya maka sunan mai sayar da Baburan da farashin da ake Sayarwa kuma idan an je wurin hakan za a gani, amma magana a nan ta yaya aka kasa yin maganin wadannan mutane, don haka idan na zama Gwamnan Jihar Kaduna zan tabbatar da yin maganin matsalar tsaro”, inji Jonathan Asake.
“Ba za mu zauna kawai muna cin bashi ba idan mun lashe zabe domin bashin da ake ci masu zuwa nan gaba ba za su iya biya ba”
Don haka idan an zabe ni na lashi takobin zan kirkiri hanyoyin samun kudin shigar da Gwamnati za ta yi dogaro da su.
Za mu canza lamarin tafiyar da Gwamnati saboda mu za mu ta fi da kowa ba wani bambanci ko kadan.
Sai kuma habbaka rayuwar Matasa da Mata
Domin a yanzu halin da ake ciki matasa na ganin akwai matsala a tattare da gudanar da rayuwarsu nan gaba don haka a shirye suke su tabbatar sun kwato yancinsu a ko’ina suka kasance.
“Mihimmin lamari ne za mu inganta rayuwar matasa da mata, kuma za mu yi wani abu domin ta yaya za a Sanya harkar ilimin matsa cikin wani yanayi har a Jihar Kaduna ake biyar kashi dari uku na karatun makarantar jami’a.
A Saminaka, da muka kasance wurin da ke Noma Masara da ya fi na ko’ina a fadin Afrika da Yamma da kuma Noman Citta da ake yi tun daga Kaciya inda har tsohon Gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya gina kamfanin sarrafa Citta, amma a yanzu wane hali suke ciki?
A mazabu 255 muna da wuraren kula da kiwon lafiya da a yanzu kawai sun tsaya ne a kan suna kawai domin yanayin da suke ciki abin tausayi ne kawai, don haka za mu tabbatar da yin gyara na musamman domin jama’a su samu ribar kula da kiwon lafiya.
Sarautun gargajiya da aka mayar da su can baya har aka rushe wasu za mu Farfado da wasu al’amura daga ciki.
“Ni a matsayi na na wanda ya jagoranci kungiyar da bata da wani kudin da take samu daga Gwamnati amma mun yi aiki kwarai har a lokacin matsalar cutar Korona mun yi amfani da dimbin tunanin mu mun samar da kayan abinci da sauran abubuwan amfanin da za su Tallafawa jama’a musamman wadanda suka kasance suna da matsalar samun kansu a sansanin yan gudun hijira duk mun raba masu kuma har da Hausawa da wadanda ba Hausawa ba duk sun samu don haka ni a matsayina shugaba ya zama dole ya zama mai dimbin basira da tunani”.
“Zamu yi wani tsarin da al’ummar mutanen karkara za su samu dukkan abubuwan da ake yi a cikin babban birnin Jiha, ba wai kawai a cikin Birni kawai ba”.
“Mafi yawan sansanin yan gudun hijirar da muka halarta a matsayin mu na kungiya duk muna tambayarsu ko Gwamnatin tarayya, karamar hukuma ko ta Jiha ta ziyarce ku sai su tabbatar mana babu ko daya sai dai kawai jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu kawai suke ziyarar Sansanin Gudunhijira da muka ziyara.
“Mata ne suka zamo wadanda suka iya tattalin dukiya da kuma tsimi da tanaji don haka sune a kan gaba wajen tafiyar da harkokin Gwamnatin mu,ko a kasar Ruwanda akwai yawan mata sama da kashi Hamsin a majalisa kuma abin lura a nan shi ne Ruwanda fa wata kasance da ta samu kanta a cikin Yaki amma a yanzu lamarin kasar ya canza baki daya saboda kyakkyawan shugabanci kawai”.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.