Home / Labarai / Tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina ne ke gabanmu – Gwamba Dikko 

Tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina ne ke gabanmu – Gwamba Dikko 

 

 

Daga Imrana Abdullahi

 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bayuana a ranar Juma’a 11 ga Agusta, 2023 cewa babu wani abin da gwamnatinsa ta sa a gaba kamar tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar da ke zaune  lungu da sako domin su koma barci da idanunsu biyu a rufe kamar yadda suke rayuwa a can  baya.

Gwamnan ya kuma kara jaddada shirin gwamnatinsa na hada hannu da hukumomin tsaro da ke jihar domin ganin tsaron al’ummar jihar ya kyautatu.

Malam Dikko Umaru Radda na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin babban Sufeton ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 14 da ta hada Katsina/Kaduna AIG Ahmad AbdurRahman a lokacin da ya ziyarci Gwamnan a gidan gwamnatin jihar Katsina.

Gwamnan ya yi la’akarin cewa babu inda ke samun ci gaba muddin tsaron yankin na samun tazgaro. Ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta hada hannu da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin ganin Katsinawa sun koma harkokinsu yadda ya kamata ba tare da wata barazanar tsaro ba.

Ya bukaci hadin kai da goyon bayan jami’an tsaron wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Mataimakin babban Sufeton ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta 14 ya jinjina wa Gwamnan ganin yadda a kodayaushe yake tsaye wajen ganin an tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Katsina tun lokacin da aka rantsar da shi a matsayin Gwamna a watan Mayun, 2023.

 

 

 

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.