Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da yake yi na ganin al’umma sun samu saukin rayuwa musamman a watan Azumin Ramadana mai alfarma, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Shetiman Mafara ya raba wa jama’a tirelolin kayan abinci guda 240 da nufin samawa jama’a saukin rayuwa musamman a wannan watan Azumi mai Alfarma.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon kayan Azumin toreloli 240 taron da aka yi a garin Talatar Mafara, tsohon Gwamnan ya ce wannan kokarin ana yin sa ne domin taimakawa jama’a a cikin Jihar su samu saukin gudanar da Azumin watan Ramadana a cikin sauki.
Wadanda za su amfana sun hada da magoya bayan jam’iyyar APC, Kungiyoyi, Marayu, Yan Gudunhijira da sauran dai daikun jama’a.
Da fatan Allah ya saka masa da alkairi.