Home / Labarai / Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Raba Tireloli 240 Na Kayan Azumi

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Raba Tireloli 240 Na Kayan Azumi

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da yake yi na ganin al’umma sun samu saukin rayuwa musamman a watan Azumin Ramadana mai alfarma, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Shetiman Mafara ya raba wa jama’a tirelolin kayan abinci guda 240 da nufin samawa jama’a saukin rayuwa musamman a wannan watan Azumi mai Alfarma.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da  rabon kayan Azumin toreloli 240 taron da aka yi a garin Talatar Mafara, tsohon Gwamnan ya ce wannan kokarin ana yin sa ne domin taimakawa jama’a a cikin Jihar su samu saukin gudanar da Azumin watan Ramadana a cikin sauki.
Wadanda za su amfana sun hada da magoya bayan jam’iyyar APC, Kungiyoyi, Marayu, Yan Gudunhijira da sauran dai daikun jama’a.
Da fatan Allah ya saka masa da alkairi.

About andiya

Check Also

GWAMNATIN TINUBU TA WUCCIN GADI CE – ATIKU

Daga Imrana Abdullahi A wani kokarin kara fadakar da dimbin yayan jam’iyyar PDP mutumin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.