Lamarin ya kasance abun murna da farin ciki a garin Abuja Jiya yayin da wani ko auren fari bai yi ba da ke shirin yin auren ya samu nasarar lashe makudan kudi miliyan biyar na gasar kamfanin Sumuntin Dangote.
Babban Manajan daraktan kamfanin Dangote mai kula da kamfanoni, Mista Olakunle Alake ya mika kyautar kudi ga wanda ya lashe gasar Mista Mamza Joshua Abba, a gaban dimbin jama’a.
Wanda ya lashe gasar dan shekaru 35 ya shiga cikin matukar farin ciki da ya bayyana da cewa mafarki ne ya zama gaskiya.
“An gaya Mani cewa ni ne na samu nasarar lashe gasar da samun kudi naira miliyan biyar. Na yi tsammani wasa ne. Sam ban yi tsammani ba cewa wannan gasar ta Dangote da gaske ne tun a karon farko, wannan yazo mani da bazata. Har sai da na kasa yin magana na wani tsawon lokaci”, inji shi.
Babban jami’in kamfanin mai kula da ayyukan ya bayyana cewa ya sayi kusan buhuna 200 na sumuntin Dangote lokacin da lamarin ya faru.
“Lokacin da na samu 0, wanda bayan haka na karbi sauran kalmomin da suka hada DANGOTE, na samu farin cikin kwarai, a halin yanzu ina farin ciki kuma ina son in zama mai rarraba kayan sumuntin Dagote nan ba da jimawa ba”, inji Mamza.
Banda babbar nasarar lashe gasar, wasu karin guda biyar kuma sun samu nasarar lashe miliyan daya kowannensu da kuma kyautar Firij da Talbijin da dai sauransu, duk mutane sun samu kyautar a lokacin gasar.
Babban Daraktan shiyya na kamfanin sumunti na Dangote, George Bankole, ya bayyana gasar da ake yi ta ” Bag of Goodies season 3″ da hukumar kula da hakkin masu yin amfani da kayan kamfanonin ta kasa cewa wani lamari ne na a kyautatawa al’umma daga cikin abin da kamfanin ke sanu daga rukunin kamfanonin Dangote.
Ya ce wannan gasar za ta Sanya tattalin arzikin ya samu ci gaba domin kudi za su shiga hannun masu amfani da kayan wanda hakan zai taimaka wajen bunkasar kasuwanni da kasuwanci baki daya.
“Masu amfani da kayan kamfanin da kuma masu raba kayan kamfanin da sauran yan Najeriya, za su iya zama masu miliyoyin kudi sau da yawa. Ita dai wannan gasar shugaban kamfanonin Dangote ne Aliko Dangote ya kirkiro da ita da nufin canza rayuwar yan Najeriya, musamman a wannan lokacin matsin tattalin arzikin da ake ciki a kasa”, inji shi.
Babban kamfanin sumuntin na Afrika ya dai kaddamar da wannan gasar ne a satin da ya gabata da nufin samar da wadanda za su samu miliyoyin kudi da za su Ketare siradin talauci ta hanyar shiga gasar, a Legas lokacin da kamfanin ya bayyana cewa masu amfani da kayan mutane dari 500 za su samu nasarar cin miliyan daya kowannensu,kuma wasu karin mutane 100 su kuma za su samu naira miliyan biyar ta hanyar lashe gasar a cikin watanni hudu.
Babbar Daraktan da ke kula da sayar da Sumunti ta kamfanin Dangote, Misis. Funmi Sanni ta bayyana cewa a matsayin sumuntin Dangote da ya damu da al’amuran masu hulda da shi babu wasu kudin da ake ganin sun yi yawa a ba masu huldar da shi domin su ne kashin bayan ci gaban kamfanin a koda yaushe.
Babban jami’in hukumar da ke kula da aiwatar da gasa ta Gwamnatin tarayya Mista Dauda Ahmadu Waja, bayyana gasar sumuntin Dangote ya yi da cewa an yi ta bisa tsari da tsare gaskiya, ya kara da cewa hukumar ta su na matukar farin cikin ganin masu hulda da kamfanin na cikin farin ciki da annashuwa.
An dai gudanar da gasar ne bisa sa’idanun babban jami’in hukumar kula da kalo- kalo ta kasa wanda Misis Ikwo Odiongenyi, da ke aiki a bangaren bayar da lasisi na hukumar.
Dukkan Gasar guda uku ana saran su samar da wadanda suka samu miliyoyin kudi mutane 125 a wata wata da za a cinye tsabar kudi naira biliyan daya da za a samu tsabar kudi da wasu kuma kyaututtukan daban.