Home / Labarai / Wani Uba Ya Mutu, An Sace Yayansa Biyu Da Ma’aikacin Banki

Wani Uba Ya Mutu, An Sace Yayansa Biyu Da Ma’aikacin Banki

Wani Uba Ya Mutu, An Sace Yayansa Biyu Da Ma’aikacin Banki

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga garin Funtuwa cikin Jihar Katsina na cewa masu satar mutane sun shiga unguwar rukunin gidajen Shagari da ke Funtuwa.
Masu satar mutanen sun yi awon gaba da yayan wani mutum har su biyu tare da wani ma’aikacin Bankin First Bank da ke aiki a garin Funtuwa, sai kuma wani mai aikin sa kai domin taimakawa al’umma mai suna Ali Bahago da yazo domin kawo dauki a lokacin da yan bindigar suke tsaka da abin da suka ga dama a unguwar ta Shagari a gefen garin Fintuwa cikin Jihar Katsina da a nan take wadanda ake zargi da cewa  yan bindigar suke sheka shi lahira.
Su dai maharan sun Isa wanann unguwa ce ta rukunin gidaje da ke Shagari da misalin karfe 11: 15 na daren ranar Alhamis.
Inda suka sace wani magidanci mai suna Alhaki Hassan Fari, da yayansa mata biyu tare da wani ma’aikacin Bankin First Bank mai suna Mista Alex, wanda sanadiyyar hakan Alhaji Hassan na take ya fadi matacce, lokacin da aka kawo masu harin.
 
Sai dai rundunar Yan sandan Jihar Katsina sun bayyana rashin jindadinsu game da irin yadda Bankin ya kasa samawa ma’aikatansa wurin zama inda za su samu tsaro koda kuwa wurin haya ne ba sai sun je suna haya a bayan gari ba.
 
 

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.