Home / KUNGIYOYI / WASU YAN TA’ADDAN YARBAWA SUN KWACE GIDAN REDIYON TARAYYA

WASU YAN TA’ADDAN YARBAWA SUN KWACE GIDAN REDIYON TARAYYA

Wasu ‘yan kungiyar Oodua Nation (Yoruba Agitators) sun yi garkuwa da gidan rediyon Amuludun FM 99.1 da misalin karfe 6 na safiyar Lahadi a Ibadan.

Gidan rediyon na daya daga cikin na gwamnatin tarayya da kuma hukumar gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN.
Sai dai An kama biyar daga cikinsu da sanyin safiyar Lahadi.

Rahotanni sun ce maharan sun mamaye gidan rediyon da laya iri-iri inda suka mamaye gidan rediyon tare da watsa shirye-shirye kai tsaye.

Sun rike fastoci dauke da rubuce-rubucen, “Al’ummar Oodua ta zo ta zauna”, “Yoruba ba su karkashin tarayyar Najeriya”, majalisar dinkin duniya kwanan nan za ta ayyana kasar Oodua” da sauransu wadansu kalaman da suke rubuce kamar yadda suka yi su.

Babban Manajan gidan rediyon, Mista Stephen Agbaje, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

“Wasu gungun masu tayar da kayar baya sun zo da daddare, suka kwace tashar, amma jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.  Sun samu nasarar kwato tashar, kuma an kama wasu

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.