Home / Labarai / Wata Alkaliya A Kaduna Ta Bayyana Yadda Aka Kashe Danta A Kasar Cyprus

Wata Alkaliya A Kaduna Ta Bayyana Yadda Aka Kashe Danta A Kasar Cyprus

Imrana Abdullahi

Wata Alkaliya mai shari’a a babbar kotu a Jihar Kaduna Mai shari’a Aminat Ahmad Bello, a ranar Litinin ta bayyana irin yadda aka kashe danta mai shekaru 25 da yaje karatu kasar Cyprus.

inda yake karatu a wata jami’a a kasar amma wadansu mutane suka halakashi a cikin kasar.

Kamar yadda uwar yaron take bayyanawa shugabar hukumar kula da huldar yan Nijetiya da mutanen da suke a kasashen waje Uwargida Abike Dabiri Erewa, Uwar yaron ta shaidawa hukumar cewa dan nata sun yi magana da shi a kafar sadarwa ta whattsapp inda ya ce mata ” mama ni dai a barni in dawo gida kawai domin wurin nan ba wurin zama bane domin akwai hadari zan iya rasa Raina,bayan hakan ne kawai sai lamarin ya zama gaskiya”.

Uwar yaron ta ce bayan ta Isa Cyprus ne ta samu gawar yaron ba wani ko wata alamar an ji masa rauni ko wata alama a jikinsa sai dai Gawa kawai.

Da take mayar da jawabi bayan ta karbi takardar koke daga uwar yaron Misis Abike Dabori Erewa ta ce duk da yankin arewacin na Cyprus bata da huldar jakadanci da Nijeriya domin bata a yarjejeniyar Majalisar dinkin duniya suk da haka za a bi ta kasar Turkiyya domin ganin an kwato yancin wannan dalibi da aka halaka.

Dabiri Erewa ta kuma yi kira ga iyayen yara da su guji kai yayansu arewacin Cyprus saboda babu hulda da Nijeriya ko kuma tsarin yarjejeniyar majalisar dinkin duniya.

Ga dai hotonsa nan da a yanzu sai dai tarihi sakamakon raba shi da rayuwarsa da aka yi a Cyprus.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.