Home / News / YA DACE DAN TAKARAR PDP YA FITO DAGA YANKIN AREWA – GWAMNA TAMBUWAL

YA DACE DAN TAKARAR PDP YA FITO DAGA YANKIN AREWA – GWAMNA TAMBUWAL

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambiwal, ya bayyana cewa lokaci ya yi da jam’iyyar PDP za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewacin Najeriya.

Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da cikakken lisaafin da ya tabbatar da cewa ya dace PDP ta natsu ta tabbatar da yin tariyar lissafin baya wajen yin lissafin irin mutanen da suka yi shugabancin Najeriya a tsawon shekaru 34 na mulkin Dimokuradiyya, za a ga cewa mutanen Kudancin kasar nan sun tserewa na yankin Arewa da shekaru a kalla hudu.
Ga dai lisaafin lokutan da kowa ne yanki ya yi ya na jan ragamar mulkin Najeriya ” zamanin Olusegun Obasanjo, ya yi shekaru Takwas sai kuma Goodluck Ebele Jonathan da ya yi shugabancin Najeriya na tsawon shekaru Shida, shi kuma marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’aduwa ya yi shekaru biyu ne sai mulkin ya koma hannun Jonathan,saboda haka idan an yi lissafi za a ga cewa yankin kudu ya tserewa yankin Arewa da shekaru hudu kenan ya na gudanar da mulki a Najeriya don haka lokaci ne da PDP za ta yi karatun ta natsu ta tabbatar da tsayar da dan takarar shugaban kasa daga arewacin Najeriya”, inji Gwamna Tambuwal.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.