Home / Labarai / Yadda Batun Kamen Almajirai Ya Gudana A Jihar Kaduna

Yadda Batun Kamen Almajirai Ya Gudana A Jihar Kaduna

Yadda Batun Kamen Almajirai Ya Gudana A Jihar Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi

Shugaban hukumar kula da ababen hawa da kuma dokar muhalli Mejo Garba Yahya Rimi mai murabus, ya bayyana cewa har yanzu ba su samu iyayen wani yaron almajiri  da mota ta buge a kan titin da ya zagaye garin Kaduna ta Yamma ba.

Ya dai bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Kaduna.

Mejo Garba Yahya Rimi wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa domin ganin an yi amfani da tsare tsaren kiyaye doka da ka’idar cutar Korona a Jihar Kaduna, ya shaidawa wakilinmu a lokacin tattaunawarsu cewa yawan Alkaluman wadanda suka kwashe a makarantar Islamiyya ta Shaikh Dahiru Bauchi da kuma masu yawon barace barace a kan tituna ya haura daga 140 zuwa 162.

Ya ce kwamitin da yake wa jagoranci zai samo wadansu kwararru da za su taimaka masu .

musamman wajen yin magana da yaren wadansu yaran da aka samu da basa jin yaren da ake magana da shi a nan kasar na Hausa ko Turanci domin samun damar aikasu zuwa kasashensu ta hanyar hukumar kula shige da ficen jama’a ta kasa.

Kamar yadda ya ce akwai wadansu daliban da aka samu a makarantar Islamiyyar da suka fito daga kasashen Bokinafaso, Nijar da Jamhuriyar Benin, kuma dukkansu za a hannanta su ga hukumar kula da shigi da ficin mama’s bayan an kammala tantancewa.

Ya dai bayyana rasuwarsa da cewa a kwanaki 5 zuwa shida da suka gabata an samu wani yaro almajiri da mota ta buge kuma har yanzu ba a samu inda iyayensa suke ba.

Saboda haka ya ci gaba da cewa babi wata Gwamnatin da za ta amince da hakan na faruwa a Jiharta.

Mejo Rimi, ya kara da cewa ba wai suna yin wannan ga wani ko nau’in wadansu mutane ba ne kawai, ” ba wai Shaikh Dahiru Baichi ba, ana yin aikin ne bisa doka kawai”.

Saboda haka kafin mu fara wannan aikin Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i ta kafa kwamiti kuma an ba mu irin yadda zamu gudanar da aikinmu don haka da hakan ne muke yin aikin.

A wani lokacin da ya gabata Gwamnonin arewa 19 da wakilin ministan babban birnin tarayya Abuja sun yi taro a Kaduna sun kuma cimma yarjejeniyar cewa duk wani almajirin da aka samu za a dauke su zuwa Jihohinsu domin ba su damar zuwa makarantun Islamiyya a wuraren da suke tare da iyayensu wanda hakan zai ba su damar komawa gidajen iyayensu idan sun tashi daga makaranta kuma muna yin amfani da wannan dokar ne.

Kuma ya bayyana cewa dokar da muke yin amfani da ita “akwai dokar Jihar kaduna da aka yi a shekarar 2016 da ta hana yawon barace barace a kan tituna ko yawace yawace a duk cikin Jihar Kaduna.

“Don haka kusan duk abin da muke yi a kan wadannan dokokin ne. Amma wasu mutane na cewa muka yi ne a kan Shaikh Dahiru Bauchi wannan ba gaskiya ba ne

“Tun da farko da muka samu kama Almajirai 22 da suka shiga daga wasu jihohi zuwa wasu Jihohina cikin kasar nan, a wannan lokacin ne muka samu nasarar kama wasu almajiran 140 kuma mun ajiyesu a sansanin Alhazai na kasa da ke Jihar Kaduna wanda doka ta amince da hakan .

Su yan makarantar Islamiyya sun wuce 160 sun kai 162 a halin yanzu saboda lambar kara karuwa take amma akwai wasu guda biyu da basa iya gaya mana sunan garin da suka fito.

“Saboda haka ne muke kokarin samun wadansu kwararru domin su taimakemu domin musan saga ina suke, saboda dole sai wadanda suke jin yarensu domin ba ma jin abin da suke fadi a yanzu”.

“Lambar za ta ci gaba da karuwa saboda wannan aikin zai ci gaba ne daga nan har tsawon watanni uku, kuma za a yi shi ne a dukkan kananan hukumomi 23 na Jihar.

 “ Saboda haka ba a garin Kaduna ba ne kawai za a yi wannan aikin”.

A game da irin tsawon kwanakin da daliban dan aka kama za a ajiyesu a sansanin Alhazai na Kaduna kuwa? Ya ce muna nan muna tantancesu kuma daga mun gama zamu daukesu zuwa Jihohinsu na asali.

“Kuma ba wai dukkansu ba ne yan Nineriya, wasunsu sun zo ne daga kasashen Nijar,Borkinafaso da Janhuriyar Benin.za kuma mu mika su ga hukumar kula da shige da ficin jama’a domin sanin ko sun zo cikin Nijeriya ta hanyar doka ko a’a.

“Mun samu nasarar daukar yara guda 140 daga gidan da suke kira Islamiyya, daga wani wuri da kuma ko suna da wani wurin kuma hakika ba mu Sani ba.

 “Jihohi Goma sha tara 19 tare da babban birnin tarayya Abuja duk sun cimma yarjejeniya cewa duk wani mai yawon yin bara ba tare da iyayensu a wurin ba da sunan yana makaranta a kama shi a kuma mayar da shi Jiharsa ko karamar hukumarsa ko kuma Mazabarsa.

 “Kuma a maganar masu yawon baraace barace akwai doka a kan hakan da ta hana aikata irin wannan a kan tituna, saboda haka duk wanda aka kama za a yi masa hukunci dai-dai da irin yadda wancan tsari ya tanadar, wato wanda Gwamnoni suka tanada a lokacin taronsu”.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.