Home / Labarai / Yadda Gwamna Aliyu Ke kokarin Mayar Da Talauci Tarihi A Jihar Sakkwato

Yadda Gwamna Aliyu Ke kokarin Mayar Da Talauci Tarihi A Jihar Sakkwato

A abinda ake gani martani ne na sauri ga matsalolinda suka addabi kasa,nunawa manya daga ciki tsakanin a fannin tattalin arziki, a fayyace matsalar talauci, Gwamna Ahmad Aliyu ya kaddamar da gagarumin tsarin rage talauci a fadin jihar,ta hanyar nada gogaggiyar tauraruwa kuma jajirtacciyar yar rajin kare hakkin Bil Adama, Barista Saadatu Yunusa Mohammed amatsayin mai bada shawara ta musamman awannan bangare.
Ana kallon yunkurin sabon  gwamnar amatsayin wani kyaykkyawa kuma  jarumin taku gaba a yaki da matsalar da ta zama babban  kalubale ga shugabancin kasa awannan lokaci, musamman ayankin Arewa, inda jihar take jagorantar shiyyar Arewa maso Yamma , kamar yadda wani rahoto ya nuna a shekarar 2023.
Haka nan kuma, zabin mai bada shawara kaman Barista Saadatu, kwararriyar lauya mai tarin basira da  ra’ayin kawo sauyi hade da tarihin gwagwarmayar kare hakkin jama’a da tallafawa matasa da matasa galihu bayan shekaru aikin hidimar al’ummar kasa na nuna lallai da gaske gwamnatin take gun aiwatar da  abin da ta shelanta tun da farko.
Sharhin jaridar “Business Day” na uku ga watan Yuli ya fassara hakkin talauci da “Yanayin da abin hannun  mutum daya ko gida suka kasa samar masa da abind a ake bukata don matsakaiciyar rayuwa tsakanin jama’a. Afadin jaridar, “Ana auna yawan talauci ne da yawan samu da kuma ratar samu tsakanin mutanen.
Sauyi a talauci nada rukunai biyu: runkunin bunkasan samu da na sauyi a rashin dai – daiton abin da ke shigowa hanu.
Yan Najeriya na fuskantar rashin dai -daito a bangaren kiwon lafiya, ilmi, samun muhalli, rashin aiki da kuma rashin samun ingantaccen tsaro.
Rahoton hukumar tattara bayanai ta kasa NBS na 2019 ya bayyyana kashi 40.1 na yan Najeriya a cikin  talauci ko mutum 4 a cikin 10, inda suke kashe kasa N137,430  duk shekaru.
Kenan mutanen miliyan Yamanin da biyu( 82.9), in ka cire jihar Borno,na rayuwa a talauci kuma za su kai miliyan casa’in( 90 ) nan da 2022 sakamakon tsadar kaya da ya Karo mutum miliyan biyu tsakanin 2020 da 2021.
Shima binciken kungiyar Nairametrics na 2022 ya nuna jihohin Sakkwato, Bayelsa da Jigawa nada jimillar mutanen miliyan sha hudu da dubu dari takwas (14.8 ) masu fama da talauci kuma ya ambanci kiwon lafiya, ilmi, rashin wadatar abinci da kayan makamashin girki a cikin manyan sabubban ko dalilan talauci a kasar.
Cikin mutane miliyan arba’in da biyar da dubu arbain da tara( 45.49) matalauta Arewa Jihar Sakkwato na dauke da miliyan daya da dubu dari takwas( 5.8) da ke fama da rashi ta fuskoki dabam-dabam da gwargwadon maki  0.409 a ma’aunin MPI.
Barista Saadatu kenan tayi susa a gurin da ke kaikayi da fadin ta a wajen kaddamarwa
“Tsarin da kushe talauci namu zai bada fifiko ga kiwon lafiya da walwalar da ta kamata.
Zamu karfafa samar da ingantacciyar kulawa da lafiya, musamman ga marasa galihu.
Wannan zai kunshi fadada kayayyakin aiki a bangaren da wadatar da magani da ci gaban matakan hana faruwar cututtuka.
 Bugu da kari, zamu karfafa kafofin bada kariya kamar yadda ya kamata ta hanyar tallafawa wadanda aka danne, tsofaffi, nakasassu da yara masu gararamba”, inda ta kara da cewa “Magance talauci ba abu ne mai sauki ba, amma kuma wajibi ne da ba za’a kyale ba”.
A yayin da Gwamna Aliyu yake tafiyayyen akanta mai dimbin kwarewa a gudanar da harkokin al’umma, wanda ya zabo ta bashi  shawara nada gogewa da hikimomi mabanbanta a fannoni da dama da suka shafi rayuwar mutane kamar yadda kudirinta na nemo tallafin abokan hadaka daga cikin hukumomin gwamnati, kungiyoyin taimakon jama’a, yan kasuwa da al’ummar kasa da kasa ke nunawa.
Daga Muhammad Bashir

About andiya

Check Also

Sanata Barau Jibrin  Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe A Tudun Biri, Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike

Daga Imrana Abdullahi Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau  Jibrin, ya jajantawa iyalan wadanda harin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.