Home / Kasuwanci / YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR CANJIN KUDIN DA AKE CIKI A YANZU – TAFIDAN BIRNIN MAGAJI

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR CANJIN KUDIN DA AKE CIKI A YANZU – TAFIDAN BIRNIN MAGAJI

..Aba ajent kudi su je Kauyuka su ba Jama’a

Daga Imrana Abdullahi

Alhaji Hassan Umar Dan Galadima, tsohon Mukaddashin babban Manajan Bankin Polaris ne ya bayyana cewa duk da batun canza kudi abu ne mai kyau da Gwamnati ta fito da shi, amma kuma abu ne da yake tattare da dimbin matsaloli da yawa.

Hassan Umar Dan Galadima wanda kuma shi ne Tafidan Birnin Magaji da ke Jihar Zamfara ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawarsa da manema labarai inda  ya ce kamar yadda kowa ya Sani a duk fadin duniya ba wanda zai iya bayar da abin da bashi da shi domin ba mai iya bayar da babu, saboda haka idan kudi bai wadata a Bankuna ba saboda ba a ba su kudin isassu ba, ba za su iya bayar da kudin ba.

“Kuma idan a haka za a ci gaba da tafiya sai da mutum ya cire naira dubu Ashirin a Injin ATM ko a kan Kanta, ba ranar da za a daina ganin layuka a Bankuna domin kudin bai wadata ba. Kuma a duba batun mutanen yankunan karkara saboda haka ma su nawa ne keda Bankuna a karkara? musamman kuma ga matsalar tsaro ko babu ma matsalar tsaro da.misalai a Jihar Zamfara daga Gusau sai Kauran Namida, Talatar Mafara sai kuma Shinkafi su kadai ne keda reshunan Banki, idan kaje irinsu tsabre a can Birnin Magaji babu Banki, irinsu Zurmi suma babu to, da yawa wadannan idan kazo ka ce wai mutum ya cire naira dubu Ashirin a kan kantar Banki ta yaya zai Isa mutanen karkara?

Sabida haka abin da ya dace Babban Bankin Najeriya su yi shi ne tun da akwai ajensi Banki ya karfafa harkar kuma an san su an yi masu rajista don haka su yakamata a ba dama, aba kowa ne ajent ya fitar da kudi daga naira miliyan uku zuwa Biyar ya ta fi karkara a rika ba mutane dubu Ashirin ko dubu Goma amma idan aka ce ba wanda za a ba dama ya cire miliyan daya irin wadannan ajent din da Bankuna suka yi masu rajista an kuma san da su, to ba ranar da wadannan dogayen layukan za su kare a Bankuna maganar gaskiya kenan.

Idan don wai kaje ka bi layi a baka dubu Ashirin ko a ATM ka cire dubu Ashirin layin nan ba zai kare ba nan da wata shida, saboda mutane nawa ne ke zuwa Banki akwai kuma inda baka iya zuwa har sai dai idan su mutanen Babban Bankin Najeriya da sauran Bankunan kasuwanci za su je kauyuka da motocin daukar kudi na Banki abi kauyukan nan ana bayar da kudi kuma hakan ba zai taba yuwuwa a gama a nan da ranar Goma ga watan da ake ciki ba don haka mu gaya wa kanmu gaskiya. Manufar ba wai ka kawo miliyan Ashirin ba ne Banki a baka miliyan Ashirin ba a ‘a.

“Abin da ake so a koya wa mutane irin yadda za su iya ajiye kudi a Banki wannan ya na da kyau, wanda ko yaro ne zai iya tanaji wato tattali hakan ya na da kyau. Amma idan kana da miliyan Ashirin kaje ka kai Banki a bude maka asusun ajiya ya na da kyau, idan kana son naira dubu dari biyar sai ka rike wannan ta kasuwancin ka ce  gobe ko jibi sai ka kara cirewa domin abin da ba a so shi ne ka ajiye wadannan makudan kudin miliyan dari, dari biyu ko biliyan guda har su rube da yawa muna ganin wadanda kudaden sun rube domin shekara da shekaru mutum ya ajiye su a daki kuma duk wanda ya ajiye kudi isaka ba ta shiga dole ne su lalace.

Tafudan Birnin Magaji ya ci gaba da bayanin cewa kuma ai tun lokacin tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi shi ya fara kawo maganar yin amfani da kudin da ba a cikin takarda ba da ake cewa a turance “cashless policy”, kuma abin ya na da kyau saboda dole mu karfafa wa kan mu Gwiwa mu fara yin ajiya a Banki to, amma maganar gaskiya ita ce muna yin kira ga Gwamnatin tarayya cewa a karfafa wa ajent Gwiwa da dukkan Bankuna na da su domin an yi masu rajista don haka a ba su kudin su je kauyuka su rika ba mutane kuma za a iya Sanya masu idanu, wannan shi ne zai kawo saukin wannan lamarin da ake ciki, a samu saukin halin da ake ciki a yanzu kuma maganar gaskiya ita ce Bankunan na ba a ba su wadatattun kudin da za su Isa ba domin zaka ga ana jifan Bankuna saboda haka ba Bankin da zai so ya ga ana jifan ana fasa masa Gilashi bai fito da kudi ba wallahi, maganar gaskiya kenan. Ga shi an yi layi amma ya kasa fito da kudi ko wadannan yan naira dari da Hamsin na da a dan rarrage abubuwa to, babu su.

Don haka ni ina yin kira ga shugaban kasa da yake Gwamnonin mu na Arewa sun same shi kuma ya yi alkawarin zai sake duba wannan lamarin. Saboda haka muke yin kira ga mutane da ayi hakuri in sha Allahu za a cimma maslaha a game da wannan abin, amma ni ina da imanin cewa tabbas za a kara lokaci domin a cikin nan da kwanaki Goma a gama wadannan abubuwan da yawa da Bankuna sun rufe reshunan du domin ba su samun riba.

Sai kuma aka samar da batun Bankunan ajensi kuma kowa ya rungume shi muna yi wa Allah godiya, matasa da dama sun samu abin yi da wahala kaje kauye ba POS dukkuwa yadda ya kai cikin karkara kaga an samu sauki, a madadin mutum ya kashe kudin mota sai ya je Gusau, Sakkwato ko Kaduna ko ya ta fi Kano ya na son ya jire kudi sai kawai a kayansu ya bayar da dari ko dari biyu ya cire kudinsa dubu Goma ko sama da haka kaga ba laifi ba ne kuma ba Haramun ya yi ba saboda kudin motar da zai kashe aje birni an yi masa saukin hakan maganar gaskiya kenan, don haka idan ana son a samu saukin abubuwan nan wajibi ne aba ajent din da aka yi wa rajista a Bankuna suje kauyuka su raba kudin nan ko su Bankunan kasuwanci su je da motocinsu da yan Sanda su raba kudin nan kuma abu ne mai wahala hakan gara ajent din nan wanda shi ba za a san ya rike kudin nan ba a ba su dama yaje ya yi wannan aikin raba kudi a kauyuka”, Hassan Umar Dan Galadima.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.