Daga Imrana Abdullahi
A cikin wata sanarwar da ya fitar kamfanin rarraba hasken wutar lantarki shiyyar Kaduna ya sanar cewa matsalar rashin wutar lantarkin da ake fama da shi a safiyar yau dinnan ya samo asali ne daga yajin aikin da yayan kungiyar kwadago da kuma sauran wadansu kungiyoyi suka shiga.
Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana mai dauke da sa hannun Abdulazeez Abdullahi shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin da ke shiyyar Kaduna ya sanar cewa ma’aikatan da suka kasance suna tare da kungiyar kwadago ne suka sauke layukan bayar da wutar ga jama’a masu karfin KVA 33, amma da zarar al’amura sun dai – daita batun wutar lantarkinzai dawo kamar yadda aka saba.
Saboda haka kamfanin na ba dimbin jama’a masu hulda da shi hakuri bisa faruwar lamarin.
Jama’a da dama dai suna ta koken cewa wannan matsalar wutar lantarkin ta Jefa su cikin kunci saboda durkushewar sana’o’insu da suke amfani da wutar lantarki kuma ga shi babu ita sam sakamakon yajin aiki da ma’aikata suka shiga.