Home / Labarai / Yajin Aikin Yan Kwadago Ya Gurgunta Sufuri,Bankuna Da Aikin Gwamnati A Kaduna

Yajin Aikin Yan Kwadago Ya Gurgunta Sufuri,Bankuna Da Aikin Gwamnati A Kaduna

Yajin Aikin Yan Kwadago Ya Gurgunta Sufuri,Bankuna Da Aikin Gwamnati A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Al’amuran harkokin Sufurin Jirgin Sama, Kasa da kuma ayyukan Bankina da ma’aikatan Gwamnati duk sun gurgunce a Jihar Kaduna baki daya.
Hakan kuwa ya faru ne sakamakon irin halin da al’amura suka kasance tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da daukacin ma’aikatan Gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi, lafiya, ilimi da dukkan bangarorin aikin Gwamnati baki daya.
Tsamin dangantakar dai ya haifar da ala tilas ma’aikata a fadin tarayyar Nijeriya suka yanke hukuncin shiga yajin aikin kwanaki biyar da suka kira a matsayin Yakin aikin gargadi ga Gwamnatin Jihar.
Tun da sanyin safiyar yau ranar Litinin ma’aikatan suka yi ta tururuwa su na zuwa ofishin kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna domin jaddada cewa ba gudu ba ja da baya game da hukuncin da suka yanke na yin yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Tun a ranar Lahadin da ta gabata ne ma’aikata karkashin jagorancin kungiyar kwadago ta kasa suka kashe wutar lantarkin Jihar baki daya, kuma a yau ranar litinin aka wayi gari asibitoci a rufe,bankuna,gidajen mai, filayen Jirgin sama da na kasa duk an rufe su baki daya, haka lamarin yake a bangaren harkokin sufurin kungiyar NURTW ta kasa.
Sakatariyar Jihar Kaduna ma ta kasance a rufe tare da dukkan ofishin aikin Gwamnatin Jihar da Kwaduna, sai kuma asibitoci da ma’aikatun Gwamnatin tarayya da suke a Jihar sun garkame sakamakon yajin aikin da ma’aikata suka shiga.
Shugabannin kungiyar kwadago daga Jihohi da tarayya duk sun yi jawabai karkashin jagorancin shugaban kungiyar kwadago ta kasa Kwamared Ayuba Waba, inda suka tabbatarwa da duniya cewa irin abin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi wa ma’aikata tun daga matakin kananan hukumomi zuwa Jiha ba adalci a ciki, sannan sun zargi Gwamnatin Jihar da bayar da alkalumman da ba na gaskiya ba a fannoni daban daban.
Sun dai ce sun lashi takobin cewa za su ci gaba da aiwatar da Yakin aikin na gargadi tsawon kwanaki biyar da suka ce in ba su samu biyar bukata ba za su shiga yajin aikin sai illa masha Allahu da nufin kawo karshen Sallamar ma’aikata a Jihar Kaduna

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.