Home / Ilimi / Yan Aji 3 Na Karamar Sakandate Za Su Koma Makaranta A Kaduna

Yan Aji 3 Na Karamar Sakandate Za Su Koma Makaranta A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa yan aji uku na makarantar karamar Sakandare a Jihar Kaduna za su koma makaranta domin rubuta jarabawar hukumar jarabawa ta Kasa da ake cewa ( NECO BECE)
Kwamishinan ilimi na Jihar Kaduna Dokta Shehu Usman Muhammad ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun.
Dokta Shehu Usaman ya ce za a rubuta jarabawar ne a ranar Litinin 23 ga satan Agusta 2021 zuwa ranar Litinin 6 ga watan Satumba 2021.
Sanarwar ta ci gaba da cewa an bayar da umarni ga makarantun sakandare su dawo karatu na yanakaranta aji uku na karamar sakandare kawai daga ranar Laraba 18 ga watan Agusta 2021 ana kuma bayar da umarni cewa a gayawa yan makaranta su koma makarantar a cikin fararen kaya kawai.
Ana kuma umartar makarantun su bi wannan umarni sau da kafa”, inji sanarwar.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.