Home / Labarai / Jama’a Su Nemi Makamin Kare Kansu

Jama’a Su Nemi Makamin Kare Kansu

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga jama’ar Jihar da su samu makamin da za su kare kawunansu daga garin yan bindiga na babu gaura ba dalili da ke neman zama ruwan Dare a duk fadin Jihar.
Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da mai bashi shawara a kan kafofin yada labarai Malam Abdu Labaran Malumfashi ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
Masari ya ci gaba da cewa daukar wannan mataki hakika zai taimaka wajen ganin an samu saukin ayyukan yan bindiga a Jihar.
Binciken da wakilin mu ya gudanar a Jihar Katsina ya shaida mana cewa akwai yawaitar kai hare haren yan bindiga tare da daukar jama’a a cikin wannan watan har ma a wuraren da suka kasance birane ne a Jihar a yanzu yan bindigar sun fara kai hari ga jama’a.
Binciken dai ya gano cewa a wurare irin na Unguwannin Mazoji a karamar hukumar Matazu da kuma Yan Tumaki a karamar hukumar Dan Musa sun fara fitowa zanga zanga su na cewa ba sa son jagorancin APC sakamakon ki san da ake yi masu tare da kwace masu Dukiya ta hanyar biyan kudin fansa.
Da yake karin bayani Malam Abdu Labaran ya ce bayar da wannan umarni ba gazawa ba ce domin jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a ko’ina ba kasancewa akwai garuruwa da yawa a kowa ce karamar hukuma.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Aims for 500,000 Barrels Daily by July, eyes stock market debut

Also the chairman Aliko Dangote has equally announced intentions to list the refinery on the Nigerian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.