Home / Labarai / Yan bindiga: Gwamna Matawalle Ya Nemi Taimakon Jamhuriyar Nijar Domin Tsare Kan Iyakoki

Yan bindiga: Gwamna Matawalle Ya Nemi Taimakon Jamhuriyar Nijar Domin Tsare Kan Iyakoki

Mustapha Imrana Abdullahi
 ….Ya yi alkawarin taimakawa da ababen hawa domin yin sintirin hadin Gwiwa
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya yi kira a game da samun hadin kai tsakanin Nijeriya da Nijar domin kawo karshen duk wani ayyukan yan Ta’adda tsakanin kasashen biyu.
Gwamna Matawalle ya yi wannan kiran ne bayan kammala taro da shugaban kasar jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a fadar shugaban da ke Niamey, sun dai tattauna batun yadda matsalar ta’addanci ke damun kasashen biyu.
Taron da shugabannin biyu suka yi an yi shi ne domin tattauna batun matsalar tsaro musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da jamhuriyar Nijar da nufin samo hanyoyin warware su baki daya, da nufin samun taimakon kasar Nijar da kuma Jihar Zamfara.
Gwamna Bello Matawalle ya kuma bayyana jin dadinsa bisa yadda shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya bashi da Jihar Zamfara damar tattauna batutuwan kula da harkokin tsaro, musamman batun satar mutane, satar Dabbobi da kuma matsalar yan bindiga a yankin Maradi da kuma wani yanki na Zamfara,Katsina da Sakkwato.
Ya kuma shaidawa shugaba Mohamed Bazoum a kan irin matakan da Gwamnati Jihar ta dauka a kokarin ganin karshen matsalar tsaro a yankin.
Gwamnan ya kara da bayanin cewa ban da shirin samar da zaman lafiya da kuma tattauna domin dai-daitawa tsakanin Juna, wannan Gwamnatin samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro a kan yadda za a lalubo masu bayar da bayanan sirri ga yan bindiga da wadanda suke hada baki su na aikata mugun aiki.
Ya ce Gwamnatinsa ta samar da na’urar daukar hoto ta CCTV domin a rika duba yadda ake gudanar da harkoki da dukkan motsin jama’a a hedikwatar Jiha da nufin ganowa da kuma bin sawun maboyar batagari da dukkan ayyukansu.
Gwamna Bello Matawalle ya ce Gwamnatinsa za ta taimaka da motoci kirar Hilux ga Gwamnatin kasar Nijar guda biyar domin a samu sahihin tsarin matakan tsaro a kan bodar Maradi da kuma sauran wasu sassan jamhuriyar Nijar da suke kan iyaka da Zamfara,Katsina da Sakkwato.
Gwamnan ya ci gaba da cewa sababbin motar kirar Hilux za a mika su ne a hannun Gwamnan Jihar Maradi a wajen wani taron da za a yi bayan samun amincewar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Ya kuma roki cewa ya na da muhimmanci a rika yin taro a kai – a kai tsakanin ministan tsaron Najeriya,Gwamnan Maradi da Gwamnan Zamfara da kuma Gwamnonin Katsina da Sakkwato da nufin samo bakin zaren a game da kalubalen tsaron da ake fuskanta tsakanin kasashen biyu.
Da yake mayar da jawabi shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum godiya ya yi wa Gwamna Matawalle bisa wannan ziyarar da ya kawo da nufin kawo karshen matsalar da ke addabar kasashen biyu,musamman a kan iyakar Maradi da yankin arewacin Najeriya maso Yamma.
Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya shawarci Gwamna Matawalle ya ci gaba da aikin da ya Sanya a gaba da nufin kawo karshen matsalar tsaron tsakanin kasashen biyu, sai ya bayar da tabbacin cewa a koda yaushe a shirye suke su bayar da taimakon da ya dace fa Gwamnatin Jihar Zamfara da nufin yaki da matsalar tsaro.
Shugaba Mohamed Bazoum ya roki Gwamnonin Najeriya da su tabbatar da kaddamar da hana shigowa da Babura (mashin) cikin Najeriya.
Shugaban kasar Nijar ya bayyana batun matsalar yan bindigar da cewa dukkan matsalar da ke zuwa Nijar na zuwa ne daga Madara da Bayan Dutsi wanda sanadiyyar hakan ya watsu zuwa Najeriya ta yankin Maradi,amma da wannan tallafin da goyon baya daga Najeriya da Gwamnatin Matawalle, hakika lamarin zai zamo tarihi.
Taron ya samu halartar ministan tsaro da harkokin cikin gida na jamhuriyar Nijar da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, da kuma shugabannin tsaron Nijar da suka hada da shugaban yan Sanda.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.