Home / Big News / Yan bindiga Na Neman Miliyan 30 Su Saki Kanwar Dan majalisa Tafoki

Yan bindiga Na Neman Miliyan 30 Su Saki Kanwar Dan majalisa Tafoki

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Katsina, musamman daga garin Tafoki na cewa yan bindigar da suka sace Kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin Jihar Katsina Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki su na neman a ba su kudin fansa na naira miliyan Talatin (30,000 000) kafin su sake ta.
Yan bindigar sun sace Asma’u Dalhatu wadda kanwa ce ga dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Tafoki, Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki.
Dan majalisa Shehu Dalhatu Tafoki ya shaidawa manema labarai cewa yan bindigar sun sace Kanwar ta sa ne da safiyar ranar Lahadi lokacin da suka kaiwa garin Tafoki hari.
Yan bindiga dai sun addabi wasu Jihohin arewa maso Yamma wanda Jihar Katsina ke ciki, inda ake samun matsalar satar jama’a a kusan kullum.
Za dai mu ci gaba da kawo maku karin bayani a nan gaba.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.