Home / Labarai / Yan bindiga Sun Sace Kanwar Mataimakin Shigaban Majalisar Dokokin Katsina

Yan bindiga Sun Sace Kanwar Mataimakin Shigaban Majalisar Dokokin Katsina

 

Mustapha Imrana Abdullahi

Wadansu yan bindigar da sula kai Hari garin Tafoki a karamar hukumar Faskari cikin Jihar Katsina sun sace kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin Jihar Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki.

 

Wadda aka sacen dai mai suna Asma’u Dalhatu, an sace ta ne da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Yan bindigar sun sace ta ne lokacin da suka kai wa garin Tafoki hari a karamar hukumar Faskari cikin Jihar Katsina

 

Mataimakim shugaban majalisar ne da kansa ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce wadanda ake zargin cewa yan bindigar ne sun kai hari garin ne da misalin karfe 1 na ranar Lahadi kuma suka ta fi kai tsaye zuwa gidan mai garin wanda nan ne babban gidansu baki daya suka kuma sace yan uwansa biyu.

 

 

Ya ce lokacin da suke kokarin shiga daji, sai barayin suka hadu da masu aikin sa kai nan da nana sai aka yi musayar wuta, wanda dalilin hakan wata daga cikin yan uwan dan majalisar ya samu kubuta, ta kuma dawo gida lafiya kalau.

 

Mataimakin shugaban majalisar ya ce an kai rahoton faruwar hakan ya jami’an tsaro.

Amma dai har yanzu yan Sanda a Jihar ba su ce komai ba game da lamarin

Kuma ya zuwa yanzu yan bindigar ba su yi magana ba game da lamarin ko kuma maganar karbar kudin fansa ba.

Shi dai wannan hari na garin Tafoki na zuwa ne kasa da Awoyi 24 da wasu yan bindiga suka kai Hari garin Kurami da ke karamar hukumar Bakori, inda sula sace mata da yayan dan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Bakori, Dokta Ibrahom Kurami.

.
Bakori dai na kimanin nisan kilomita 42 ne zuwa Faskari inda yan bindigar suka sace mutane kashi na biyu

Jihar Katsina dai a cikin yan kwanakin nan na fama da yawaitar satar jama’a da suka hada da yan uwa,iyalai na yan siyasa da kuma dimbin mutanen gari

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.