Home / Labarai / Yan bindiga Sun Sace Yayan Wani Mai Unguwar Sabuwar Kasa Guda 4

Yan bindiga Sun Sace Yayan Wani Mai Unguwar Sabuwar Kasa Guda 4

Mustapha Imrana Abdullahi

Kamar dai yadda mutanen garin suka shaidawa wakilinmu cewa yan bindigan sun kai hari a garin Sabuwar kasa ne da ke karamar hukumar Kafur da sanyin safiyar ranar Litinin sun kuma yi awon gaba da iyalan Alhaji Hamza Umar, Sato sun ta fi da yayansa guda hudu.

Alhaji Umar dai shi ne mai unguwar Sabiwar kass, kuma shugaban bangaren mulkin karamar hukumar Funtuwa da ke Jihar Katsina arewacin Najeriya.

Amma ya zuwa yanzu har yau jami’an tsaro ba su ce komai ba game da hakan.

Yayan Kantoman rikon karamar hukumar Funtuwa da aka sace sun hada da

1. Aliyu Hamza Nasarawa
2. Aisha Hamza Nasarawa
3. Ibrahim Hamza Nasarawa
4. Fatima Hamza Nasarawa.

Da fatan Allah ya yi mana maganin faruwar lamarin amin, su kuma ya kubutar da su cikin Aminci da salama.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.