Home / Labarai / Yan bindiga Sun Kai Hari Jami’ar Greenfield Da Ke Kaduna

Yan bindiga Sun Kai Hari Jami’ar Greenfield Da Ke Kaduna

Yan bindiga Sun Kai Hari Jami’ar Greenfield Da Ke Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da ke fitowa daga Jihar Kaduna na cewa wadansu yan bindiga sun kai hari a Daren jiya ga jami’a mai zaman kanta ta Greenfield da kan hanyar Abuja daga cikin garin Kaduna.
Bayanan da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar na cewa maharan sun kashe wani mutum daya a makarantar mai suna Paul Ude Okafo da ke aiki a jami’ar.
Bayanan da kwamishinan ma’aikatar kula da tsaro da  harkokin  cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya fitar na cewa an dauke wadansu daliban da ya zuwa yanzu ba a san ko su nawa ba ne.
Samuel Aruwan ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro na can su na gudanar da ayyukansu domin dai- daita al’amura a jami’ar da ke a Kasarami kan titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Chikun.
Fatarmu dai shi ne Allah ya raba nagari da mugu a koda yaushe.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.