Home / Labarai / Yan bindiga Sun Kashe Mutane A Kaduna

Yan bindiga Sun Kashe Mutane A Kaduna

Yan bindiga Sun Kai Hari A Wani Coci 
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna ta mika sakon ta’aziyyarta ga wadansu mutane mabiya addinin Kirista da aka kaiwa hari a cikin Coci lokacin da suke bauta.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa yan bindigar sun kuma kashe mutane 6 a karamar hukumar Birnin Gwari, an kuma kashe wani a karamar hukumar  Kachiya,an kashe mai shekaru Bakwai a karamar hukumar Igabi.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi Allah wadai da harin da wasu yan bindiga suka kai wani wurin bauta a ranar Lahadi a kauyen Manini, karamar hukumar Chikun.
A cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwa da aka rabawa manema labarai, ta bayyana cewa jami’an tsaro wasu yan bindiga sun kai hari kan wadansu masu bauta a cikin Cocin Haske Baptist da ke Manini, da misalin karfe 9:30 na safe, kuma sun kashe mai bauta, mai suna Dokta Zechariah Dogonyaro.
Kamar yadda rahoton ya ce an kuma yi awon gaba da wasu masu bauta guda hudu. An kuma yi wa wani mutum mai suna Shehu Mainika rauni a duk wannan kewayen
A wani rahoton kuma da Gwamnatin ta karba daga jami’an tsaron sun ce yan bindiga sun kai hari kauyen Bagoma a karamar hukumar Birnin Gwari an kashe mutane 6 ha sunayensu kamar haka.
1 – Bala Gwamna
2- Kasage Ali
3 – Mai Jakki
4 – Makeri Kugu
5 – Haruna Kawu
6 – Ali Agaji
An kuma yi wa wani mutum daya rauni mai suna Salisu  Gwamna yayan Bala Gwamna an yi masa rauni.
An kuma bayar da wani rahoton cewa yan bindigar sun kai hari a kauyen Amfu a karamar hukumar Kachiya, inda aka tabbatar da sun kashe wata mata mai suna Rahila Dauda.
Sai kuma wani bayanin kokarin kona Gawar wani dan shekaru Bakwai mai suna Abubakar Sarki Musa da aka samu a cikin wani ginin da ba kammala ba a hayin Danmani, karamar hukumar Rigasa.
Inda wani mai suna Saddique Umar, mai shekaru 18 ya amsa cewa shi ya aikata aika aikar bayan ya kaishi daji da nufin kwace masa wayar hannu.
Gwamna Nasiru El- Rufa’i ya bayyana bacin ransa da faruwar wannan lamarin na daukar rayukan jama’a haka kawai.
Haka kuma ya bayyana kisan da aka yi wa masu aikin bautar da cewa wani aiki ne na shedan, sai ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga Cocin Haske Baptist bisa rashin da aka yi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu ya kuma ba wadanda suka samu raunuka sauki.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.