Home / Labarai / Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1 Sun Sace Mutane 20 A Kaduna

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1 Sun Sace Mutane 20 A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna n bayanin cewa sama da mutane 20 ne aka sace, aka kuma kashe mutum 1 a lokacin wani harin da aka kai a unguwar Danbushiya da ke wajen harabar rukuni gidaje na Millenium City, a karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Wani Shaidan gani da ido ya shaidawa wakilinmu cewa yan bindigar sun zo wurin da lamarin ya faru ne da misalin karfe 9: 30 na daren ranar Lahadin da ta gabata suka kuma kafa wani shinge a kusa da Gadar unguwar Danbushiya da ta hada su da unguwar Keke.

Shaidan gani da idon wanda ya bayyana sunansa da Malam Isa ya ce maharan tun da farko sun fake ne kamar su jami’an tsaro ne amma suka gabatar da harin da suka yi niyyar kaiwa jama’a.

“Da misalin karfe 9: 30 na daren, Naga mutane a cikin kakin soja da kayan yan Sanda a kusa da wannan Gada suna binciken ababen hawa da suka hada da Babura da kuma masu tafiya a kasa. Sai daga baya suka tattara jama’a suna yi kamar suna bincikar wadanda suke bada hadin kai da dokar Sanya Takunkumin rufe Fuska.

“Amma sai na fara tunanin samun shakka a zuciya ta, kamar wadannan ba jami’an tsaron gaskiya bane musamman a lokacin da suka fara daga murya ga masu ababen hawa su fara kwanciya a kasa,  a wannan lokacin ne suke tsare duk wani mutum da ke tafiya a kasa. Sai suka daina zaben mutanen da suke bincika”.

” Sai suka fara shiga da mutane cikin wani ginin da ba a kammala ba, sauransu kuma suka tsaya a kan titi suna ci gaba da tafiya da mutane a cikin ginin lokacin da suka fara yi wa jama’a kururuwa suns Ihu ga mutane, lokacin nan ne na boye, sun dai kai su Goma sha biyar kowa dauke da bindiga”, Inji Isa.

Ya kuma bayyanawa majiyarmu cewa jami’an tsaro ba su zo da sauri ba, kuma koda suka zo ma sun yi ta bude masu jiniya daga nesa wanda dalilin hakan yasa maharan suka gudu abin su kafin su zo”.

Malam Isa dai ya tabbatar wa majiyarmu cewa daya daga cikin wadanda aka kama ya samu tsarewa a lokacin da suke kokarin shiga da su cikin Kangon ginin, sskamakon hakan wani shima yaso ya gudu amma nan take suka kashe shi.

Wani mazaunin wannan wuri da ya bukaci a boye sunansa ya ce ya tsallake rijiya da baya ne saboda ya tsaya domin ya saya wa yaransa a da ke gida abubuwan bukata

Kamar yadda ya bayyana ” Bayan na yi sayayya domin yaya na, sai wani ya kira ni ya shaida Mani abin da ke faruwa a unguwar mu”.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan Sandan Jihar Kaduna ASP M9hammed Jalige ya yi alkawarin tuntubar babban baturen yan sanda DPO na yankin rukunin gidaje na Millenium City.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.