Home / KUNGIYOYI / Al’Ummar Atyap Sun Yaba Wa El- Rufa’i Bisa Taron Zaman Lafiya

Al’Ummar Atyap Sun Yaba Wa El- Rufa’i Bisa Taron Zaman Lafiya

Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar kabilar Atyap na kasa Furofesa Lucius I Bamaiyi ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna bisa yin taron tabbatar da zaman lafiya.
Furofesa Lucius Bamaiyi ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da kungiyar ta yi a Kaduna, inda ya ce hakika sun ji dadin taron da Gwamnan ya jagoranta domin a ci gaba da samun zaman lafiya a tsakanin kabilu da daukacin al’ummar Jihar Kaduna baki daya.
“Zamu ba Gwamnan goyon baya da cikakken hadin kai domin cimma wannan manufa ta zaman lafiya, saboda abin da Gwamnan ya yi abin a yaba ne kwarai”.
Ya ci gaba da cewa muna yin godiya bisa irin wannan kokari na Gwamnan saboda irin abin da muke ta kokarin yi kenan tsawon lokaci har aka samu shekaru ba tare da an samu wata matsalar tashin hankali ba a daukacin yankin Atyap baki daya.
“Ko a shekarar 2011 ba a samu tashin hankali a yankin Atyap ba ko kadan, kuma ko a cikin satinnan mun yi gagarumin taron zaman lafiya a Gora da Gidan Kaya domin a samu zaman lafiya”.
A game da rahoton binciken rikice rikicen da aka yi a kuwa wanda Gwamnatocin baya suka kafa kwamitoci karkashin Usman Mu’azu da Rahila Kojo kuwa yayan kungiyar sun ce an samu nasarar aiwatar da wadansu bukatun da aka cimma wanda a ciki har da na samar da Masarautar Atyap da kuma samar da Hakimi da mazabar Zango da hausawa suke samar da Kansilan yankin a duk lokacin zabe.
Kuma abin da ake jiran Gwamnati ta aiwatar shi ne kammala wurin Noman ranin da al’ummar Atyap da na hausa Fulani za su yi amfani da shi domin Noman rani, kuma an cimma matsaya cewa dukkan bangarorin za su yi amfani da wurin Noman ranin ne baki daya.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.