Home / Labarai / Yan Boko Haram Sun Bulla A Jihar Nasarawa

Yan Boko Haram Sun Bulla A Jihar Nasarawa

Yan Boko Haram Sun Bulla A Jihar Nasarawa

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Bayanan da ke fitowa daga Jihar Nasarawa ta bakin Gwamna Abdullahi Sule na cewa a halin yanzu Gwamnati ta gano cewa yayan kungiyar Boko Haram suna yin sansani a cikin Jiharsa ta Nasarawa, wanda sakamakon hakan ake kara samun matsalar tsaro a cikin Jihar.

 

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

 

Gwamnan, ya ce wadannan yan Ta’adda suna cikin wadanda ke kara haifar da matsalar tsaro a cikin Jihar, indai za a iya tunawa yan ta’addan an Koresu ne daga mafakarsu inda suka yi sansani a Toto Kafin yanzu daga baya su sake kara harhaduwa a kan ziyarar Nasarawa da Banuwai suna kuma kai hare hare a kan mutane duk lokacin da suka ga dama.

 

Injiniya Abdullahi Sule wanda shi ne Gwamnan Jihar Nasarawa ya ce wasu daga cikin yan Boko Haram da ke ta’addanci a Nasarawa yayan kungiyar ne mai bangare da suna Darussalam da aka taba kora daga Jihar Neja an kuma samu nasarar kama wadansu dari 900 tare da hadin Gwiwar jamai’an tsaro.

 

Ya ce kasancewarsu yan kungiyar Boko Haram an tabbatar da shi ne sakamakon su da kansu da suka fadi cewa lallai yayan kungiyar ne, inda ya ce suna iyakar kokarinsu domin magance matsalar, wannan ne yasa muka zo muka shaidawa shugaban kasa halin da ake ciki.

 

Ya ce tattaunawar da suka yi da shugaban kasar ya shafi batun matsalar tsaro ne kawai, wanda mai yuwuwa Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kula da titin Jitata, wanda shi ne ake amfani da shi mafi sauki da ya hada Jihar da babban birnin tarayya Abuja.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.