Home / Kasuwanci / Yan Kasuwar Kaduna Na Cikin Tagumi

Yan Kasuwar Kaduna Na Cikin Tagumi

Daga Imrana Abdullahi
Kamar yadda aka Sani cewa cutar Korona Bairus ta addabi duniya baki daya, yasa Gwamnatin Jihar kaduna daukar irin matakin nan da ake cewa Gurguwar tsanya da wuri tare fara yin Tula domin kaucewa irin abin da ka iya zuwa a gaba.
Daukar matakin kaucewa shiga yanayin yaduwar cutar Korona da ake wa lakabi da Convid – 19 ya haifar da rufe kasuwanni domin gujewa samun cinkoso jama’a, haka nan Gwamnatin Jihar kaduna ta gargadi a kan taruwar mutane cikin masallatai da Coci Coci inda a yanzu an samu sati biyu wato Juma’a guda biyu da ranakun Lahadi biyu ba a sallar Juma’a ko majami’u a ranar Lahadi duk domin gujewa cinkoso jama’a da ka iya haifar da yaduwar cutar.
A bangare daya kuma Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i na cewa hada yaduwar cutar ne abin da ya dace da yi domin babu isassun asibitoci ko cibiyoyin kula da masu fama da cutar Korona Bairus, balantana Likitoci da sauran jami’an kula da kiwon lafiya  idan sun kamu.
Amma kuma daukar wannan mataki domin hana yaduwar ciwon da alamu ya Jefa wadansu mutane da yawa cikin halin matsala kasancewar sai talaka ya fita sannan ya samu abin da zai sa a bakinsa tare da sauran iyali.
Yan kasuwar Jihar kaduna ma na komawa a cikin irin wannan yanayi na yaki da cutar Covid – 19 wato Korona bairu saboda kamar yadda suka shaidawa wakilinmu an rufe kasuwanni musamman babbar kasuwar kaduna da dimbin jama’a kan yi kasuwanci su samu abinci.
A yau ranar Talata 7 ga watan Afrilu,2020. Da Gwamnatin ta dan daga wa mutane kafa na kwanaki biyu domin su fita su sayi kayan abinci da sauran muhimman kayan bukatu ya kasuwar na kokawa kwarai kan yadda suka samu kansu na tsayawa cirko cirko a bakin kasuwar suna yin tagumi wanda kamar yadda suka shaidawa wakilinmu cewa sun yi tsammanin Gwamnati za ta bude masu kasuwar ne domin suma su samu a kwanaki biyu da aka Sassauta dokar su samu na kaiwa iyalansu da sauran bukatu yau da kullum da suka hada da rashin lafiya da sauransu.
” Amma abin mamaki sai aka ki bude kasuwar ga shi kuma muna cikin wani hali na matsi tare da iyali”.
A nata bangaren Gwamnatin Jihar Kaduna na cewa ta sassauta dokar hana fitar ne na kwanaki biyu domin jama’a su samu sayen kayan abinci da na sauran bukatun yau da kullum a kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Ya zuwa rubuta wannan rahoton wadansu yan kasuwar na nan suna ci gaba da tsayawa a gefen kasuwar wadansu kuma tuni sun kama gabansu amma duk rai a bace.
Sai dai da wakilinmu ya zagaya wajen masu sana’ar kayan abinci da kuma kayan miya ya gansu suns ta hada hadar saye da Sayarwa inda yannkayan miya ke kulla Tumatiri a cikin Leda mai ruwan Dorowa suns Sayarwa da jama’a.
A bangare daya kuma akwai batun tsadar kayan Masarufi na yau da kullum da wasu yan kasuwa ke tsauwalawa mutane tsadar da suka ga dama domin samun damar hana fita dare da rana da Gwamnatin ta saka a Jihar baki daya.
Za kuma mu kawo maku irin korafe korafen da suka dabaibaye rabon abincin da Gwamnati ke yi gida gida a nan gaba kadan domin a yanzu muna bin wuraren da ake wannan rabon domin ganewa idanu yadda lamarinnke gudana.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.