Home / Labarai / Yan Nijeriya Na Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

Yan Nijeriya Na Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

Yan Nijeriya Na Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal
Abdulmumin Giwa Ne Ya Rubuto
Yan Nijeriya daga kowace kusurwa, lungu da sako na fadin kasar suna murnar ta ya Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal muranar ranar haihuwarsa da ya yi bikin ranar haihuwar a ranar Lahadin da ta gabata.
Tambuwal da ya cika shekaru Hamsin da Biyar (55) a ranar 10 ga watan Janairu, na shekarar 2021 ya samu sakonni masu tarin yawa daga dukkan bangarorin kasar nan, suna yi masa addu’ar samun tsawancin kwana domin ya ci gaba da yi wa kasa da jama’arta aiki, sakonnin dai sun zo ne daga kafofin Sada zumunta  na zamani daban daban, abin ban sha’awa.
Yan siyasa, shugabannin addini da kuma manyan yan kasuwa na cikin yan Nijeriya wadanda suka ta ya Gwamnan murnar ranar haihuwarsa. Wanda aka bayyana a matsayin shugaba mai aiki tukuru, hangen nesa abin dogaro kuma ayi ko yi da shi domin ya yi an gani an kuma shaida kwazonsa.
Domin mutum ne da ya yi aiki tukuru wajen samar da damarmaki da yawa ga jama’arsa da kuma kasa baki daya a jimlace.
Koda yake Gwamna Tambuwal ya zabi da ya yi murnar ranar haihuwarsa ta hanyar yin addu’o’i ga kasa baki daya da ke fuskantar kalubale da yawa kala kala, yan Nijeriya da dama sun hadu tare domin ta ya shi murnar ranar haihuwar ta kafofi daban daban da suka hada da jaridu da dama.
Gwamnan na Jihar Sakkwato wanda a halin yanzu shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin PDP na Nijeriya ya kasance dan takarar shugaban tarayyar Nijeriya da ya nemi jam’iyyar ta tsayar da shi karkashin PDP.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.