Home / Labarai / Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Da Sassan Jikin Mutum A Kaduna

Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Da Sassan Jikin Mutum A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Rundunar Yan Sandan Nijeriya ta kasa reshen Jihar Kaduna sun yi nasarar kama wadansu mutane biyu da sassan jikin mutum a tare da su.
Su dai wadannan mutane biyu da aka bayyana sunayensu kamar haka Abdul Aziz Jimo dan shekaru 68 da Muhammad Isa mai  shekaru 30 da suke zaune a layin Zaki unguwar Kabala ta Yamma cikin garin Kaduna, an same su ne a makabaratar Musilmi da ke Unguwar Kudenden, bayan da jami’an yan Sanda suka samu wani kira  waya cewa an ga mutane a makabartar Musulmin inda nan da nan babban baturen yan Sanda DPO da ke kula da Kakuri ya himmatu zuwa wajen.
Bayan da jami’an Yan sandan suka Isa wurin sun yi nasarar kama wadannan mutane biyu da ake zarginsu da aikata tsafi, an dai kama su ne a ranar 24 ga watan Afrilu 2021.
An kuma samu mutanen da Fatanya da wasu sassan jikin mutane.
Kamar dai yadda sanarwar da rundunar yan sandan mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mohammad Jaligi ya sanyawa hannu ta sanar cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma in an kammala za a gabatar da su gaban kotu.
Rundunar ta kuma bayyana cewa ta na yin maraba da duk wani ingantaccen sahihin bayani daga jama’a na duk wasu da ba a amince wa take taken su ba a cikin al’umma.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.