Home / Labarai / Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashi Mutane 13 A Katsina

Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashi Mutane 13 A Katsina

Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashi Mutane 13 A Katsina
Mustapha Imrana Abdullahi
Rundunar yan Sanda ta kasa reshen Jihar Katsina ta bayyana nasarar kama wadansu mutanen da suka addabi Jihar da fashi da makami da sauran aikata miyagun ayyukan su 13.
Rundunar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da ta bake kolin wadanda ake zargin gaban manema labarai a hedikwatarsu da ke cikin garin Katsina, a ranar 24, ga watan Disamba, 2020.
Mota kirar Toyota Corolla da yan Sanda suka gano kenan
Yan sandan sun kama mutane 13 bisa zarginsu da aikata fashi da makami da suka shahara wajen addabar yankin unguwar Turawa (GRA) cikin garin Katsina.
An dai samu nasarar kama su ne lokacin da aka kai samame maboyarsu biyo bayan samun sahihan bauanai, da suka tabbatar cewa suna cikin aikata wadansu aikin Fashi da makami da dama a Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar yan Sandan Jihar Katsina Gambo Isah, ya bayyana hakan a lokacin wani baje kolin masu laifin ga manema labarai a Katsina.
 Inda ya tabbatarwa manema labarai cewa wadanda ake zargin suna tsallake Katangun ko shingayen gidajen jama’a musamman ga yadda binciken ya nuna a unguwannin GRA wanda a halin yanzu har sun sace motoci uku kala daban daban, kuma a halin yanzu yan Sanda sun yi nasarar gano guda biyu.
Kamar yadda wani mai suna Isa ya bayyana, akwai wani Muhamamd Garba sun hada baki da wani Sirajo Mai – Akuya wanda a yanzu ake nemansa suna sace mota kirar Toyota Corolla mai dauke da lamba kamar haka BS 428 KW.
 Ya ci gaba da cewa wadanda ake zargin suna kan hanyarsu ta zuwa Kano tare da motar da suka sace, sai wani mutum da ya san wanda yake da wannan motar sai ya sings binsu a baya.
Kakakin rundunar yan Sandan ya ci gaba da bayanin cewa mutum ya yi ta binsu har zuwa garin Bichi karamar hukumar Bichi a Jihar Kano inda ya bayyana alamar cewa ga abin da ke faruwa, wanda hakan ya yi sanadiyyar kama mutanen biyu da suke cikin motar.
Kakakin rundunar ya kuma ce a wani wuri kuma na daban jami’an rundunar sun yi nasarar kama wadansu da suka shahara wajen zama dilolin Tabar Wiwi a Katsina an kuma samu nasarar ne  a ranar 12 ga watan Nuwamba sun kuma hada da wani mai suna Hayatu Rabi’u da salahuddin Salisu.
Hayatu Rabi’u da Salahuddin Salisu an kama su ne da wadansu kunshin da ake zargin tabar wiwi ne.
Kuma dukkansu sun amsa laifinsu a lokacin da ake gudanar da bincike, wanda da haka ne jami’an YanSandan za su dauki mataki kamar yadda dokar kasa ta tanadar.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.