Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane biyar yan gida daya sakamakon tashin wani abin fashewa da ya tashi a kauyen Yammama a karamar hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.
Mai.magana da yawun rundunar yan sandan SP Gambo Isa ne ya tabbatar da hakan
Babban baturen yan sanda DPO da ke Malumfashi ya kawo rahoton cewa wani ABU mai kara mai karfi ya fashe a cikin Gonar wani Alhaji Usaini Maikwai.
Isa ya bayyana cewa nan da nan DPO din ya jagoranci wadansu jami’an zuwa wurin da lamarin ya faru, da ake zargin wani abu ya fashe.
Kakakin rundunar yan sandan ya tabbatar da mutuwar wadansu yara na Alhaji Adamu Yammama, kuma ya ce abin fashewar ya kuma raunata mutane 6 da suke zaune a karkashin Itace.
Ya ce kwararrun jami’an tsaro a kan batun abubuwan fashewa na EOD da CID tuni suna can suna gudanar da bincike.