Home / Labarai / Yan Ta’adda Na Cin Karensu Ba Babbaka A Faskari – Isa Bilbis

Yan Ta’adda Na Cin Karensu Ba Babbaka A Faskari – Isa Bilbis

Daga Abdullahi H Sheme

Yan Ta’adda Na Cin Karensu Ba Babbaka A Faskari – Isa Bilbis
An yi kira ga Gwamnatin tarayya da  Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari da ta hanzarta kawo dauki ga al’ummar karamar hukumar Faskari kafin yan Ta’adda su karar da su baki daya.
Alhaji Isa Bilbis ya ce yin kira ga Gwamnatin tarayya, Gwamnatin  jihar katsina ya zama wajibi saboda a halin da ake ciki tamkar Gwamnati ba ta ma san abin da ke faruwa ba a yankin karamar hukumar Faskari baki daya.
“Batun satar mutane na neman zama ruwan Dare kusan kullum sai an dauki mutane ana Garkuwa da su, ga barazana ga rayukan jama’a iri iri, rashin kwanciyar hankali da jama’a ke fama da shi dare da rana safiya da maraice domin komai na iya faruwa da mutum a koda yaushe”, inji Bilbis.
 Alhaji Bilbis ya ci gaba da cewa akwai muhimmanci kwarai ga Gwamnatin tarayya da Gwamnatin Jihar Katsina da su  kara daukar mataki wajen kawo karshen rashin tsaron da ya addabi wadansu yankunan jahar musamman yankin karamar hukumar faskari
 Alhaji Isa Balarabe Bilbis Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da manoma na jahar katsina ya yi wannan kiran  lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Funtuwa cikin Jihar Katsina.
 Alhaji Isa Balarabe ya ci gaba da cewar “babu shakka wannan rashin tsaron ya durkusar da dukkan harkokin kasuwancin yankin sannan babu wata rana da ‘yan ta’addar ba za su kai hari musamman a yankin Bilbis, ko a ‘yan kwanakin nan ‘yan ta’addan sun kashe mutane da yawa kuma sun dauki wasu yanzu haka su na hannun ‘yan ta’addar Shugaban ‘yan kasuwar da manoman na jahar katsina Ya kara kira ga Gwamnatin tarayya da ta yima Allah ta dubi yadda ‘yan ta’addan suke kashe al’umma su kuma  yi garkuwa da wasu kuma sukone masu dukiyarsu ya ci gaba da cewar Idan Gwamnatin ba ta yi da gaske ba Noma ba zai yuwu ba a wannan shekarar saboda a halin yanzu manoman yankin ba su da ikon zuwa sharar Gonakinsu  ko a kai takin gargajiya gona”, Inji Isa Bilbis.
Alhaji Isa Balarabe Bilbis ya ce ya san yadda Gwamnatin jahar katsina ta damu da wannan ta’addancin da a ke aikatawa a wasu sassan jahar sannan ya yi kira ga dukkan Al’ummar musulmi da su tashi tsaye wajen gudanar da addi’o’i musamman a wannan watan na Ramadan mai albarka.
 Alhaji Isa ya ya bawa jami’an tsaron yankin yadda suke kokari ya ce yakamata Gwamnatin tarayya da ta samar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma a yankin sabon garin Bilbis.
” A gaskiya a karamar hukumar faskari an yi asarar rayuka hade da dukiyoyin Al’umma yanzu haka kauyuka da yawan gaske sun zama kufai jama’a suna cikin wahala kuma ba su da abinci don haka masu hannu da shuni su ci gaba da taimakonsu daga karshe shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da manoma na jahar Kuma Shugaban kungiyar Afgasan ta kasa shiyyar jahohin Arewa maso yamma ya yabawa ‘ya’yan kungiyar yadda suka hada kansu wajen ciyar da kasa gaba da kuma samarma kasa isasshen abinci.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.