Home / Labarai / Yan bindiga Sun Sace Mutane 12 Lokacin Sallar Dare A Katsina

Yan bindiga Sun Sace Mutane 12 Lokacin Sallar Dare A Katsina

Yan bindiga Sun Sace Mutane 12 Lokacin Sallar Dare A Katsina

 Rahotannin da muke samu daga Jihar Katsina na cewa Yan bindiga sun Sace mutane 12 lokacin da suke Sallar dare ta Tuhajjud da ake yi a kowane Goma na karshen watan Ramadana  a wani  bayan garin Jibiya cikin Jihar Katsina.

Kamar yadda wani mazaunin  wurin mai suna Fahd Muktar ya shaidawa majiyarmu ta kafar yada labaran Channels mai wallafa labaranta  a yanar  cewa hakika wannan lamari ya faru ga yan uwansa, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare kuma daga isarsu sai kawai suka rika yin harbi a cikin isaka na kan mai uwa da wabi.

Kuma sun sace mutane 12 da suke yin Ibadar sun shige da su cikin daji.

Muktar ya ci gaba da bayanin cewa daman tun da dadewa sai da aka gargadi mutanen da ke wurin kan yuwuwar faruwar irin wannan harin

” Karin zuwan na su dama sai da aka yi wa jama’a gargadin bayanin zuwan nasu a kafafen Sada zumunta na whatsapp, inda aka rika gayawa jama’a cewa mai yuwuwa za a kawo masu hari da misalin karfe sha biyu na dare”, inji Malam Muktar.

” Addu’armu kawai shi ne Allah ya dubi halin da muke ciki a Jibiya ya kawo mana dauki. Wannan harin na faruwa ne a kullum don haka ba sabon abu ba ne”.

Don haka muke kira ga masu daukar nauyin wannan hare haren da su tuna cewa akwai ranar da za a tsaya gaban Allah”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa akwai irin wannan matsalar ta kai hare hare da dama da yan bindiga ke aikatawa, inda ya ce akwai lokacin da aka kai wani hari aka Sace mutane 40 gida 28 sula samu kubuta

Wani mazaunin wannan wurin mai suna Muhammafu Sani ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce hakika an Sace mutane 40 da ke gabatar da Ibada.

Idan muka samu wani karin bayani ko ta bangaren jami’an tsaro geme da lamarin zaku ji dag wajen mu, in Allah yaso.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.