Home / News / YAYAN APC RESHEN JIHAR KANO SUN DAUKI MATAKAN SASANTAWA A TSAKANINSU

YAYAN APC RESHEN JIHAR KANO SUN DAUKI MATAKAN SASANTAWA A TSAKANINSU

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Yobe shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC da ke kokarin shirya babban zaben jam’iyyar na kasa, Honarabul Mai Mala Buni tare da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar da kuma sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun zauna wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na APC daga Jihar Kano.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da Darakta Janar mai kula da harkokin kafafen yada labarai Mamman Mohammed, ya sanyawa hannu.

Taron tattaunawar dai ya mayar da hankali ne ga batun yadda za a dai- daita da kuma kara habbaka jam’iyyar a Jihar.

Bayanin da muka samu ya tabbatar da cewa a karshen taron, dukkan mahalarta taron sun jinjinawa Juna tare da bayyana gamsuwa da irin yadda taron da abin da ya fito daga bayan taron.

Taron a karkashin jagorancin shugaban rikon APC na kasa Gwamna Mai Mala Buni ya na daga cikin matakan da aka dauka a jam’iyyar domin dai- daitawa tsakanin yayan jam’iyyar da suka dade su na tayar da hakarkari game da babban taro na kasa da za a yi nan gaba kadan.

Kwamitin na Buni ya mayar da hankali ne wajen ganin an warware matsalolin da suke gabanin babban zaben na kasa da nufin kara hada kai da dunkulewar yayan jam’iyyar wuri daya.

Janairu 25, 2022.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.