Home / News / Yayan PDP Na Murna Da Sake Duban Shari’ar Shugaban Kasa A Kotun Koli

Yayan PDP Na Murna Da Sake Duban Shari’ar Shugaban Kasa A Kotun Koli

Daga Imrana Kaduna
Wanda ya samar da kungiyar Deservation.org, kuma Darakta Janar Dakta Sani Adamu, ya jinjinawa shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus da daukacin shugabancin jam’iyyar baki daya bisa irin yadda suka bukaci kotun koli da ta sake duba hukuncin da ta yanke a shari’a tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP Dakta Atiku Abubakar da ya shigar saboda zaben shugaban kasa da ya gabata.
In dai zaku iya tunawa dan takarar da ya tsayawa PDP takarar shugaban kasa Dakta Atiku Abubakar ya kalubalanci sakamakon zaben shekarar 2019 daga kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa har zuwa kotun koli amma dukkan hukuncin da aka yanke Jam’iyyar APC ce ta samu nasara da Muhammadu Buhari ya tsaya takara a karkashinta.
Kamar yadda Dakta Adamu ya bayyana cewa irin yadda shugabannin PDP karkashin jagorancin Yarima uche Secondus sun ba yan Nijeriya wata sabuwar dama da kwarin Gwiwar samun nasarar da kowa ke bukata.
Hakika ina yin jinjina da yin godiya ga Yarima Uche Secondus bisa irin yadda ya dauki wannan matakin da ya dace a dauka tun da dadewa amma dai a yanzu ma muna marasa da matakin da aka dauka.
Jigon na Jam’iyyar PDP da ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan ya fahimci cewa an dauki wannan matakin a sake duba irin hukuncin da kotun kolin ta yanke, ya kuma bayar da shawara ga shugaban na PDP da kada ya bari munafukai su lalata zaman lafiya da dai daiton da jam’iyyar ke samu a yanzu.
Ya kara da cewa dawowar Atiku cikin PDP ya kara wa jam’iyya tare da yayanta daraja da martaba da suke amsa sunansu a ko’ina
Ina rokon Yarima Secondus da kada ya amince da masu bakin cikin yan munafunci da ba su nufin jam’iyyar da alkairi su haifar da matsaloli musamman da suke cewa wai PDP ta canza tsarinta na shiyya shiyya.
Kamar yadda zamu iya gani, mai girma Alhaji Atiku Abubakar ya dawo cikin gidansa na PDP sai jam’iyyar ta kara farin jini tare da daukaka. Mun samu nasarar lashe zabe a Jihohin Kano, Katsina,Imo,Bauchi, Adamawa da Oyo da a can baya suke hannun APC.
Kamar yadda suka bayyana bayan tattaunawar tasu cewa PDP ta kada APC da Buhari a zaben shugaban kasa, amma kuma aka murkushe mu. Don haka muke kara yin kira ga jam’iyyar PDP da su ci gaba da rike bangaren Dakta Atiku Abubakar da Peter Obi su tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
 Mai fafutukar da yake mazaunin Abuja kuma dan siyasa ya jaddada wa shugaban jam’iyyar PDP goyon bayansa a dukkan hidimar siyasa a nan gaba.
A madadin shugabannin da ke jagorantar shirye shiryen Atiku 774 2019 da kungiyar Deservation.org, cewa jam’iyyar PDP za ta samu tabbacin cewa zamu taimaki wannan jam’iyyar mu fadakar da miliyoyin mutane a kasa baki daya domin samun nasarar jam’iyyar da kuma dan takarar shugaban kasa Dakta Atiku Abubakar.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.