Daga Imrana Abdullahi
Dokta Muhammad Sani Uwaisu FCNA, garkuwan Kudun Zazzau, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmin Duniya baki daya da su kara yin riko da abubuwan da suka koya a wannan watan na Azumi domin samun zira tare da babban rabo a duniya da Lahira.
Garkuwan Kudun Zazzau ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala taron rufe karatun wa’azin watan Ramadana na Bana da aka yi a Rigachikun lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
“Idan mun lura karatun da aka yi a wajen wannan rufe tafsirin na Bana a Masallacin tunawa da marigayi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Rigachikun karkashin jagorancin Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun duk ya ta’allaka ne ga yin biyayya ga shugabanci don haka a duk lokacin da aka ce al’umma na zaune ba tare da hadin kai da shugabanci ba lallai za a ga cewa duk karfinsu sun tarwatsa don haka a nan an koya wa al’umma sanin amfanin jagoranci su kuma shugabannin su jagoranci al’umma da adalci su kuma al’ummar su yi ma shugabannin biyayya idan hakan ta faru sai kaga al’umma na ci gaba, idan kuwa lamarin yakasance kowa na yin abin da ya ga dama ko a cikin al’umma ne idan kuwa aka kasance a cikin zaman Yan marina kowa da inda ya sa ma gaba ba tare da tunanin yin biyayya ba to, lallai wata rana za a wayi gari ta tarwatse.
“Don haka mu al’ummar Najeriya musamman mu yan arewa Musulmi muka yi amfani da wannan karantarwar in Allah yaso za a samu abin da ake nema, in kuma mun ci gaba da rayuwa a cikin irin abin da ake ciki a yanzu ba tare da shugabancin ba sai dai kawai muce wa’iyazubillahi domin ba a san abin da lamarin zai kai mu ba nan gaba.
THESHIELD Garkuwa