….Uba Sani Ne Ya Fi Kowane Gwamna Samuna Nasara A Harkar Tsaro
Alhaji Yusuf Abubakar Garba da ake yi wa lakabi da Yusuf Mai kwari, ya bayyana fitarsa daga PDP zuwa jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.
Alhaji Yusuf Abubakar Mai kwari ya bayyana cewa babu wanda ya yi masa laifi a jam’iyyar PDP da ya bari, ina dai fatan alkairi ga kowa tare da yin kira ga jama’a da suke cikin PDP da su zo domin hada hannu da shi a tafiyar Gwamna Sanata Uba Sani da ya samu gagarumin ci gaba a harkar tsaron lafiya da dukiyar jama’a da a halin yanzu sai dai ayi ko yi da abin da yake yi a batun samar da tsaro kamar yadda kowa zai iya tabbatarwa ya shaida yadda lamarin tsaron yake a Jihar Kaduna.
” A yau ranar 17 ga watan daya, 2025, ina tabbatarwa da sanar da jama’ar duniya cewa na bar PDP na koma jam’iyyar APC, wannan ya biyo bayan irin tuntubar da muka yi ta sama da ta kasa a yadda tafiyar Jihar take da kuma irin gayyata da sha’awar da aka yi na mu bayar da tamu gudunmawar a jam’iyyar APC kamar yadda kowa ya Sani irin raya kasar da ake yi a Jihar Kaduna karkashin jagoranci Sanata Dokta Uba Sani wajen raya al’ummar karkara da inganta rayuwarsu Uba Sani shi ne Gwamnan da ya fi kowa ne Gwamna samun nasara a harkokin tsaron Jiha muna godiya ga Allah da ya bayar da wannan dama sannan ina shaidawa dukkan jama’a masoyana da wadanda suka zo gidana suka nuna sha’awar hadewa da ni domin shiga jam’iyyar APC da su shiga a duk inda suke a mazabunsu su sanar da mu domin muma mu sanar da duniya”.
“Ina kuma sake godiya ga dukkan yayan jam’iyyar da na bari ta PDP sakamakon irin zaman mutunci da girmama juna da muka yi da kuma zaman lami lafiya da muka yi na Amana ina tabbatar maku cewa wallahi, ba wanda ya yi Mani laifi a jam’iyyar PDP ya sa na barta babu ko daya yanayi ne yazo da kuma muma muzo mu bayar da gudunmawar mu domin kawo ci gaba a wannan yankin da Jiha ta mu don haka ina tabbatar maku cewa muna nan tare bisa Aminci da girmama Juna kuma ina gayyatar ku da kuzo ku bi jirginmu a bi tawagar Malam Una Sani na Jihar Kaduna da ake aiwatar da ayyukan ci gaba, ina yi wa kowa fatan alkairi Allah yasa abin da muka yi shi ne mafi alkairi a gare mu da gare ku baki daya muna godiya.