Home / Labarai /   Za A Fara Karbar Kudin Ajiyar Aikin Hajji A Ranar Litinin – Hannatu Zailani  

  Za A Fara Karbar Kudin Ajiyar Aikin Hajji A Ranar Litinin – Hannatu Zailani  

Za A Fara Karbar Kudin Ajiyar Aikin Hajji A Ranar Litinin – Hannatu Zailani
Mustapha Imrana Abdullahi
Hukumar kula da aikin Hajji ta Jihar Kaduna karkashin jagorancin Hajiya Hannatu Zailani ta bayyana cewa daga ranar Litinin mai zuwa hukumar za ta fara karbar kudin ajiyar aikin Hajjin bana, wato na shekarar 2021 da ya yi dai dai da 21/12/2020.
Bayanin hakan ya fito ne daga mai rikon mukamin shugabancin hukumar Hajiya Hannatu Zailani a lokacin wata tattaunawa a Kaduna.
Hajiya Hannatu ta kara da cewa mai son zuwa aikin Hajji ana son ya ajiye kudi a kalla naira dubu dari Takwas (800,000) zuwa miliyan daya da rabi (1.5). har ya zuwa lokacin da Gwamnatin tarayya za ta fadi yawan kudin da za a biya domin zuwa aikin na Bana.
Ta kuma yi kira ga masu son tafiya aikin Hajjin da su ziyarci cibiyar yin rajistar da ta fi kusa da su a kananan hukumomin da suke tare da fasfonsu domin su karbi takardar da ya dace ta shaidar ajiyar kudi, domin yin rajista.
Hajiya Hannatu ta kuma ci gaba da yin kira ga maniyyatan da su hanzarta yin amfani da wannan damar domin yin ajiya a hankali.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.