Daga Imrana Abdullahi
An yi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da ta duba yuwuwar rage harajin da ake cajin Kamfanoni da sauran masu sana’o’i a fadin kasa baki daya domin a samu ci gaban tattalin arzikin kasa.
Alhaji Faruk Suleiman shugaban kwamitin shirya kasuwar duniya ta shekarar 2025 karo 46 da za a fara a ranar Juma’a 14 ga watan Fabrairu zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu 2025 mai zuwa insha Allahu.
“Muna kara fadakar da gwambati cewa idan ana samun yawaitar karin kudin haraji ta Dama da Hagu da ta tsakiya, lallai babu shakka ana samun matsalar abubuwa su yi wa Kamfanoni da masu shi wahala kwarai wanda sanadiyyar hakan Kamfanoni na lalacewa su rushe sakamakon hakan ana samun raunin tattalin arziki don haka muna son a saukaka wa Kamfanoni su samu sukunin tsayawa da kafafunsu”.
Tuni an kammala shirin bude wannan kasuwar ta duniya a ranar Asabar 15 ga watan Janairu 2025 da misalin karfe 10 na safiya.
Faruk ya kara da cewa sun rigaya sun tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci a ciki da wajen Najeriya da suka hada tun daga ma’aikatar ciniki da masana’antu da sauran wadanda suke hada hadar kasuwanci a ciki da wajen Najeriya domin samun gudunmawarsu a ciyar da kuma kara bunkasa kasuwar.
“Muna godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Sanata Uba Sani, bisa kokarin da take yi mana a koda yaushe na gani wannan kasuwar duniya ta kasa da kasa ta samu ci gaban da ya dace, hakika lamarin na Sanya mu a cikin farin ciki kwarai”.
Muna kara yin kira ba daukacin al’umma da cewa su shirya tsaf domin halartar wannan kasuwar duniya da za a fara a watan Fabrairu mai zuwa domin za su ga muhimman abubuwa na ci gaban da ba su taba gani ba da duniya ke alfahari da su.
Kassshe Bakwai zuwa Tara amma 7 duk suna kasa sun tabbatar da zuwan na su kasuwar duniyar
Za a samar da dimbin masu kananan sana’o’i, manya da kuma muhimman Kamfanonin da duk za su baje kolin kayan su a lokacin.