Home / Uncategorized / Za A Yi Maganin Yan Bindiga Baki Daya – Suleiman Shu’aibu Shinkafi

Za A Yi Maganin Yan Bindiga Baki Daya – Suleiman Shu’aibu Shinkafi

 

An bayyana kokarin da Ministan tsaro Dokta Muhammad Bello Matawalle, karkashin Gwamnatin tarayya ke yi da cewa aiki ne da zai kawo karshen yan Ta’adda masu satar jama’a da Garkuwa da mutane da ayyukansu ke kokarin hana Noma da ci gaban tattalin arzikin kasa.
Dokta Suleiman Shu’aibi Shinkafi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilin mu a kan Gadon Asibiti a Kaduna.
“Tun daman mun shaidawa mutane cewa ja da baya ba gajiyawa ba ne ba kuma tsoro ba ne shirin fada ne kawa da Gwamnati ke kokarin yi domin kawo karshen matsalar baki daya”.
Dokta Suleiman ya ci gaba da cewa dole ne su gaya wa mutane gaskiya kamar yadda ya dace kuma kamar yadda suka saba.
“Kamar yadda mai girma ministan tsaro ya fadi cewa an ba jami’an tsaro dukkan abin da ya kamata a ba su domin su aiwatar da aikin da ya dace, kasancewar lamarin ya harzuka su domin barin yan ta’addan nan na aikata abin da suke so ba karamin nakasu ba ne ga wannan Gwamnatin saboda haka ne a halin yanzu aka tashi tsaye domin kakkabe yan ta’addan nan baki daya,wanda a yanzu haka an shiga Dajin Sakkwato da Zamfara da dukkan yankunan Arewa maso Yamma za a rarraba Sojoji da za su yi aiki ba Dare ba rana don haka duk inda yan Ta’adda suke sai an kakkabe su baki daya kaf sannan za a dawo, shi kansa ministan tsaron zai koma Sakkwato tare da Christopher Musa da nufin ceto Arewa, Najeriya da yankin Arewa maso Yamma baki daya domin an rigaya an ba su umarni saboda haka masu cewa wai akwai hannun gwamnati a ciki su tsaya su yi kallo Suga abin da zai faru domin a yanzu aiki ne gadan gadan”.
” Ina tabbatar wa jama’a cewa duk wani dan Ta’adda zai yaba wa Aya zakinta domin nan ba da dadewa ba za a kawo karshen lamarin jama’a za su huta domin yawan wannan kashe kashen zai kawo karshe

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.