Daga Imrana Abdullahi
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta sanar da ranar 15, ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin lokacin da za a gudanar da zaben shugabanni da Kansilolin a suk fadin Jihar.
Shugaban hukumar Lawal Faskari ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Katsina da ya samu halartar wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro a Jihar.
Ya ce an yi wannan sanarwar ne domin tabbatar da abin da doka ta tanadar a harkar zabe.
A lokacin zaben kananan hukumomin ana saran samun zaben shugabannin kananan hukumomi 34 da Kansiloli 361 a daukacin kananan hukumomi 34 na Jihar.