Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
An yi kira ga daukacin al’umma baki daya da su tashi tsaye wajen bayar da gudunmawarsu domin a kawar da matsalar lalacewar tarbiyya wadda ta haifar da wasu matasa suka dauki halayyar yi wa jama’a kwacen wayoyin hannu.
Shugaban karamar hukumar Funtuwa da ke Jihar Katsina Malam Lawal Sani Matazu ne ya bayyana hakan a lokacin da muke tattaunawa da shi ta wayar Salula.
Lawal Sani Matazu ya ci gaba da cewa lamarin tsaro fa harka ce da ta shafi kowa saboda haka ana bukatar kowa ya bayar da gudunmawarsa domin a tsaron lafiya da dukiyar jama’a ya inganta.
“Kowa sai ya tashi tsaye a cikin al’ummar da yake ya bayar da gudunmawa a game harkar tsaro da nufin samun ci gaban jama’a”.
“Kowa ya rika kwaba wa yayan da suke a kusa da shi koda ba nasa ba ne da ya Haifa. Domin da can haka lamarin yake kowa zai iya yi wa dan wani fada a duk lokacin da ya ga yaro na yin wani abu kuma koda dan nan ba nasa ba ne, amma yanzu lamari ya lalace saboda wasu na gudun kada ace sun yi wa dan wani magana abin da ya haifar wa al’umma suka shiga cikin wani mawuyacin halin kakanikayi duk dalilin gurbacewar tarbiyya ya kawo hakan”.
Saboda haka sai kowa ya tashi tsaye a tabbatar da yin gyara a koda yaushe