Home / Ilimi / ZA MU MAGANCE MATSALAR HIZBURRAHIM FUNTUWA – SARKIN MUSULMI

ZA MU MAGANCE MATSALAR HIZBURRAHIM FUNTUWA – SARKIN MUSULMI

 

Daga Hussaini Yero, Funtua

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya dau Alwashin magance matsalar Makarantar Madarasatu Ziburahim karkashin jagorancin zawuyar Shek Abubakar Alti Funtuwa da ke cikin Jihar Katsina.

 

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin bikin yaye dalibai mahadata Al’kur’ani da saukar sa a yau Lahadi a cikin garin Funtuwa.

 

A jawabinsa Mai alfarma sarkin Musulmi ya jinjina wa  Malaman Makarantar da duk Shekara suna samun mahaddata Al’kur’ani mai tsarki da kuma wadanda suka sauke shi .shekuru uku ke nan Makarantar bata samu damar yin bikin mahaddatan ba sakamakon annobar Korona,amma cikin kudira Allah ayau dalibai 800 ne suka sauke Al’kur’ani da mahadata ashirin.Inji Mai alfarma Saadu Abubakar.

 

‘Mai alfarma sarkin ya jinjinwa hazikan Malaman Makarantar wace ta shekara sama da sitin da kafuwa.kuma ta yaye Manyan mutane akasar nan masu mukamai daban daban Babban abun alfahari mu shine Shugaban alkalin alkalai na Jihar Katsina shine Shugaban tsafin dalibai na Makarantar Mai shiria Musa Danladi.kuma shi da kansa ya ke jagorantar kiran masu jawabai a wannan biki.wannan ya tabbatar mana da cewa, Hizburrahim Funtuwa , Makaranta ce wace ya kamata a taimakamata wajan cigabanta na ko wane sashe,dan haka na gamishu da yadda hukumar Makarantar ke tafiyar da ita kuma tsawon shekaru shida na ke jagorantar cigaban Makarantar na gamsu da yadda ake tafiyar da ita kuma da yardar Allah zamu zauna da hukumar Makarantar dan gain mun samu hanyoyin samun nasara cigaban ta.inji Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Saadu Abubakar.

 

Shugaban Makarantar Ustaz Salisu Tasiu Funtuwa yayi tsakaci ne akan tarihin Makarantar Madarasatu Hizburrahim Funtuwa,wace ta fara ne daga Makarantar allo ta koma tsarin Islamiya ,kuma ta shekarunta sitin ke nan da kafuwa ,tana da Rasa da dama da cikin Jahohin Katsina, Kaduna,Kano da Zamfara.kuma yanzu haka akwai shashen kuliya da kuma bangare koyan sana’a dan dalibai su dagara da kan su.

Kuma yanzu haka daga wannan Makarantar muyaye dalibai da dama da suka fita kashen waje dan karo ilimi.
A karshe .

Akarshe Shugaban Makarantar yayi mika godiyar sa ga Uban Makarantar Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Saadu Abubakar da ya dauki gabara tafiya da makarantar.da kuma masu taimakawa Makarantar dan ganin cigabanta.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.