Home / Ilimi / Za’A Magance Matsalar Yawan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta A Najeriya – Dokta Ardo

Za’A Magance Matsalar Yawan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta A Najeriya – Dokta Ardo

Daga Imrana Abdullahi

 

Dokta Umar Ardo, darakta ne a hukumar kula da yayan makiyaya ta kasa ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta wajen ci gaban harkokin ilimi a duk fadin tarayyar Najeriya da nufin ciyar da kasa tare da al’ummarta gaba.

 

 

Dokta Umar Ardo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna

Ya ce a matsayinsa na wanda ke aiki domin ci gaban ilimi “hakika ma’aikatar ilimi na yin aiki domin ci gaban ilimi bisa taare tsare da tanaje tanajen wannan Gwamnatin”.

 

 

Dokta Ardo ya ci gaba da cewa babban dalilin zuwansu a garin Kaduna shi ne domin tattauna batutuwan ciyar da ilimin yaya mata gaba ta hanyar samar masu ingantaccen ilimi, amma kuma sai muka duba cewa hakan ba zai yuwu ba sai da ingantattun malamai da kayan aiki, kuma yayan da ba su makaranta yaya za a yi a dawo da su”.

 

 

Dokta Ardo ya kara da cewa kiyasi ya nuna a Najeriya muna da yara sama da miliyan Goma da dubu dari biyar da ba su zuwa makaranta a halin yanzu.

” a cikin wannan kason akwai yaya mata kashi 63 daga cikin yawan wannan kaso na miliyan Goma da dubu dari biyar ba su zuwa makaranta”.

 

Ardo ya ce an kuma gano cewa hakan na faruwa ne bisa ga dalilai da yawa da duka hada da al’adu, rashin Sani, talauci da sauran abubuwa da yawa, wanda hakan ya sa yaya mata ba su zuwa makaranta.

 

 

Hakazalika Dokta Umar Ardo ya yi tulawar dalilan da ya sa yayan Fulani da masunta basa zuwa makaranta abin da ya ce duk da yi akalla shekaru 30 a wannan hukuma ta ilmantar da yayan makiyaya suna yin tsare tsare da kuma fitar da manhajojin Lula da ilimi da Koyar da shi saboda ilimin haske ne da kowa ke bukatar ya samu.domin shi ne ginshikin zaman duniya har mutum ya fitar da kansa daga cikin akuba.

Daga cikin wannan kiyasin da aka lissafa aka bayar da shi na wadanda ba sa zuwa makaranta akwai yayan makiyaya miliyan uku zuwa hudu da aka tabbatar ba su zuwa makaranta.

 

 

“Amma mun gano cewa akwai matsaloli da yawa da suka Sanya ba su zuwa makarantar da suka hada da bangaren yanayin rayuwar Fulani, domin iyaye sun dogara da yara ne wajen yin kiwon Dabbobinsu da kuma yin Noma suna ganin akwai kyashi kwarai wajen daukar yayansu su rika zuwa makaranta a madadin kawai ya bi Akuya,Tunkiya ko saniya.

 

 

“Kuma wani al’amarin da aka gano shi ne a lokacin da yakamata yaro na cikin aji ana karatu shi ne lokacin da su kuma yayan makiyaya suke wajen yin kiwon Dabbobi, wannan na daya daga cikin abin da ke ba mu ciwon kai wajen bayar da yaya suje makaranta, kuma yawancin iyayen ba su yi karatun zamani ba don haka ba su ma san mihimmancinsa ba.Don haka ba su damu ba su bar yayansu suje makaranta madadin zuwa kiwo,yawancin iyayen ba su da fahimta ba su da ilimi kullum sai an yi ta fahimtar da su kafin su dauki yayansu zuwa makaranta.

 

 

Kuma yawanci suna zaune a cikin dazuzzuka ne saboda haka masu ilimi ya dace su ba su ilimin sune malamai da sauran bangaren ilimi ake a rika dubawa, to, su kuma malaman suna jin kyashin shiga cikin daji su yi rayuwarsu a can. Sai kuma su makiyaya suna yawan tashi daga wuri zuwa wani wurin domin idan wani abu ya faru ko rashin abinci,ruwan sha na mutane da Dabbobinsu sai kawai su kaurace su bar makarantar a can baya don haka dole sai an duba makiyaya, mashayar ruwa da abinci idan akwai su sai a ba su makaranta, in kuwa ba haka ba za a ci gaba da samun kalubale ne kawai danga ne da ilimin yayan makiyaya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.