….Muna aiki ba Dare ba rana domin samar da zaman lafiya a tsakanin jama’a
An yi kira ga daukacin iyaye da su mayar da hankali wajen yi wa yayansu nunin a rika fadakarwa domin tabbatar da an samu zaman lafiya da kyakkyawan zamantakewa a tsakanin al’umma.
“Tun da aka nada ni wannan sarautar da kuma jakadancin zaman lafiya mu na aiki a koda yaushe Dare da rana domin haka ta cimma ruwa ta yadda al’umma za su ci gaba”.
Jakadan Zaman lafiya Alhaji Kabiru Danladi Marafan Goningora,ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Talbijin din Liberty a cikin shirin Shanshani.
Danladi ya ci gaba da cewa kira ga shugabanni ya zama wajibi su tabbatar a cikin zuciyarsu cewa zaman lafiya ya fi komai
” mu ba za mu amince ace wai za a raba kasa ba domin zamantakewar ta fi komai muhimmanci, ba za mu yi sakaci masu kokarin Jefa kasa da al’ummarta cikin damuwa su samu nasara ba”.
Marafan Goningora ya ci gaba da bayanin cewa a ranar sabuwar shekara yan uwa Kiristoci za su kawo masa ziyara har gida domin su gaishe shi a kuma Sada zumunta ta zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin juna”.