Home / Labarai / Zamfara ta ba da umarnin harbe masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba

Zamfara ta ba da umarnin harbe masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba

Daga Imrana Abdullahi

A kokarin Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta umurci jami’an tsaro da su bindige masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar sakamakon hana hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar.

Gwamna Dauda Lawal ne ya bayar da wannan umarni a ranar Asabar a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, inda ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen ayyukan barna da kuma aiwatar da matakan kare lafiya da jin dadin jama’a.

Ya jaddada cewa an bai wa jami’an tsaro umarnin daukar kwakkwaran mataki tare da harbe duk wanda aka samu yana aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

“Wannan umarni ya zama dole don tabbatar da tsaro da tsaron mutanen Zamfara da kuma hana masu aikata miyagun laifuka aikata irin wadannan ayyuka.

“Haka kuma wani mataki ne na gaggawa don baiwa Gwamnatin Jiha damar kula da dukiyar jihar baki daya tare da dakile ayyukan da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Babu shakka, hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin matsalar ayyukan ’yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara.  Dole ne mu dauki matakin gaggawa don dakile wannan barazana da dawo da zaman lafiya da tsaro a cikin al’ummominmu”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

About andiya

Check Also

Sanata Barau Jibrin  Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe A Tudun Biri, Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike

Daga Imrana Abdullahi Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau  Jibrin, ya jajantawa iyalan wadanda harin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.