Home / News / Zan Amince Da Duk Hukumcin Da Hukumar Zaɓe Ta Yanke – Hon Ibrahim Aliyu

Zan Amince Da Duk Hukumcin Da Hukumar Zaɓe Ta Yanke – Hon Ibrahim Aliyu

Daga Bashir Bello Sokoto, Najeriya
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Wurno/Raba, dake Jihar Sokoto, Honarabul Ibrahim Al-Mustapha Aliyu ya bayyana cewa zai amince da duk hukumcin da hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana a matsayin sakamakon zaɓen da aka sake gudanarwa.
Hon Ibrahim Al-Mustapha wanda ya kasance dan Jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar sa da manema labarai a garin Sokoto yayin gudanar da zaɓen cike gurbi wanda ya gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Ya kara da cewa a wancan zaɓen da aka gudanar na ranar 25 ga watan Fabreru, wasu bara – gurbin mutane sun tayar da hatsaniya a runfunan zaɓe wadanda suka san cewa yana da karfi a wajen wanda hakan yasa a lokacin da ake tattara sakamakon zabe ya sanar da hukumar zaɓe cewa duk hukumcin da suka yanke a matsayisa na dan Kasa mai bin doka, zai aminta da shi.
Ya ce, da farko an ce runfuna 12 ne amma daga baya an dawo ance runfuna 45 wanda a yanzu aka sake gudanar da zaɓe, kuma da yardar Allah muna kan gaba dukda hakan.
“Dama babban abin da ake bukata ga wanda yake wakilci shi ne ya kawo wa al’umma romon dimokuradiyya na cigaban ga abin da ya shafe su da kuma bin kididdiga da suka bada umarni ta hanyar doka na kashe kudi domin aga anyi amfani da su ta hanyar daya dace, sannan da yin dokoki domin samar da ingancin Gwamnati kuma shi ne abin da muka saka a gaba har Allah Ya taimaka muka samu nasara daidai gwargwado.
A game da batun tsaro, ya shawarci mahukuntan da abin ya shafa da a tsaya a dubi musabbabin lamarin sannan a san hanyoyin da za a iya magance ta domin a samu Ingantaccen zaman lafiya a kasar, sannan Gwamnati ta kara kaimi wajen bin duk wasu hanyoyin daya kamata don kawo karshen wannan matsalolin.
Honarabul Ibrahim Al-Mustapha, ya yi kira ga Matasa da mata da su kasance mutane masu nagarta da kuzari, masu rike amana tare da Jajircewa, kana masu ilimi da dogaro da kai domin goben su ta yi kyau.
“Mun samu matsaloli a baya dangane da ilimi wanda hakan yasa muka kara Jajircewa wajen ganin cewa mun tallafawa ‘ya’yan talakawa da wadanda basu iya yin karatu fiye da sakandare domin muga cewa sunje Jami’a sunyi karatun likitanci, zanen gine-gine da zama Injiniyoyi wanda suma zasu iya zama abun alfahari ga al’umma nan gaba.” Inji Shi

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.