Home / Big News / ZAN BAYYANA MATSAYI NA A WATAN FABRAIRU – BALA MUHAMMAD

ZAN BAYYANA MATSAYI NA A WATAN FABRAIRU – BALA MUHAMMAD

 

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed ya karbi rahoto daga kwamitin tuntubar da kuma wayar da kan al’umma game da batun takarar kujerar shugaban kasa Nijeriya karkashin jagorancin Sanata Adamu Gumba.

Lokacin da gwamnan ke magana kan aiki tukuru da kwamitin suka yi Gwamnan ya yaba wa ‘yan kwamitin bisa sadaukarwar da suka yi, wajen aiki tukuru kuma gwamnan ya nuna gamsuwar sa kan ci gaba da yi masa kiranye tare da kara masa kwarin gwiwar kan tsayawa takarar shugaban ƙasar Nijeriya a zabe mai zuwa.

Gwamnan yace kara da cewa gwamnatin PDP a jihar Bauchi da ke karkashin sa ta yi nasarar aiwatar da ayyukan raya kasa da dama duk da kalubalen tattalin arzikin da ake fama da shi, yace bambance-bambance ba zai zama tushen raba Najeriya ba. Nijeriya tana bukatar wanda zai hada kan yan kasar a matsayin kasa daya al’umma daya.

Jami’yyar mu na PDP tana da kwarewan iya shugaban ci.

A halin yanzu Nijeriya suna bukatar wanda zai jajirce kan farfado da tattalin arzikin kasa da zaran mun samu nasara zamu mai da hankali ne kan tinkar matsalar tattalin arziki yace jamiyyar su ta PDP ta tsara taswirar ciyar da Najeriya gaba kuma za a aiwatar da ita.

Idan aka samu damar.

Gwamna) Bala Muhammed ya yi alkawarin cewa za su karfafa hadin kai, wanzar da zaman lafiya kwanciyar hankali, da soyayya a tsakanin ‘yan Najeriya yana mai bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar siyasa daya tilo da ‘yan Najeriya ke fata.

Yayin da yake bayyana matsayar sa kan takarar kujerar shugaban Nijeriya a 2023 Gwamnan ya nuna matukar farin cikin kan kyautata masa zato da aka yi, ya yaba wa kwamitin domin tuntubar ya kara da cewa zai bayyana matsayinsa a watan Fabrairu.

Tun da farko shugaban kwamitin tuntuba da wayar da kan jama’a Sanata Adamu Gumba ya taya gwamnan murnar bisa irin sakamakon da, suka samu wanda ke nuni da cewa ‘yan Najeriya sun amince da ya fito takarar kujerar shugaban kasa a 2023.

Yace Dukkanin sakon da suka shiga don jin Bahsi sai su fahimci cewa mutane sun yi na’am da batun Gwamna Bala ba ya bukatar gabatarwa a ko’ina a kasar nan saboda jajircewarsa, karamcinsa, aiki tukuru da kuma imanian da ake dashi kan kazoon da kokarin sa wajen tvabbatar da hadin kan kasa da yan kasar baki daya.

Domin ci gaban Najeriya ta ko wani fanni

Karahan Rahoton Kenan Jamilu Barau Daga Bauchi

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.